An ambaci sunan wani sanatan arewa tare da wasu 204 da bashi yayi wa katutu a tsuliya

An ambaci sunan wani sanatan arewa tare da wasu 204 da bashi yayi wa katutu a tsuliya

An bayyana sunan Sanatan Najeriya, Abdullahi Adamu, da wasu mutane 204 a matsayin wadanda ke da tarin bashi wanda yayi masu katutu bayan sun amshi bashi daga bankin First Bank.

A wani rubutu da bankin ta yada a ranar Litinin, 24 ga watan Yuni, 2019 a jaridar Punch, an lissafa kamfanoni 133 a matsayin masu matsala wajen biyan bashi tare da darektocin su.

A bisa ga rubutun, kamfanonin sanatan suna dauke da basussuka na kimanin naira biliyan 2.5.

Mista Abdullahi, wanda ke wakiltan yankin Nassarawa ta Kudu a majalisar dattawan Najeriya, ya kasance daya daga cikin darektocin kamfanonin biyu masu dauke da basussuka, kamfanonin sun hada da Nagari Integrated Dairy Farms da Keffi Flours Mills Limited.

Lissafi ya nuna cewa Nagari Integrated Dairy Farm ta dauki bashi na lokaci mai tsawo a ranar 21 ga watan Yuli, 2011. Inda ta yi alkawarin biyan bashin a ranar 20 ga watan Yuli, 2016. Amman a halin yanzu, bashin ya kai naira biliyan 2.1.

Har ila yau, Keffi Flour Mills Limited ta samu bashin ne daga bankin a ranar 8 ga watan Oktoba tare da alkawarin biya a ranar 7 ga watan Oktoba, 2014. Bankin har ila yau tace fiye da naira miliyan 345 ya rage ba a biya ba.

KU KARANTA KUMA: Duniya ta zo karshe: Wani gari da ba a bari mutane suyi sallah sai sun biya kudi

A halin da ake ciki, First Bank ta shawarci kamfanoni 133, har da kamfanonin Mista Adamu, dasu hada kai da bankin don neman mafita akan basussukansu.

Sai dai jaridar Premium Times ta ruwaito cewa duk kokarin da tayi don ta bakin akan ikirarin bai samu ba. Shi da hadiminansa basu mayar da sakonnin waya da kiran waya ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel