Ta bayyana: Dalilin da yasa yan mata ke fita zance da samari
-Wani bincike da aka gudanar a jami'ar Azuza da ke a Pacific ya nuna cewa dayawan yan mata na fita yawo da samarinsu saboda su ci abincin bati
-Binciken ya bayyana cewa sakamakon da aka samu bayana nuna cewa kowacce mace na yin alaka saboda hakanan
-Binciken ya kuma nuna cewa ana samun irin wannan alaka ta 'Kiran Abinci' a tsakanin duka jinsina ba wai mata kawai ba
Wani sabon bincike da aka gudanar ya bayyana cewa kashi daya bisa uku na yanmata na fita zance da samari saboda abincin bati.
Brian Collison, Jennifer Howell da Trista Harig na jami’ar Azuza da ke Pacific ne suka gudanar da binciken, kuma suka buga sakamakon binciken a mujallar kimiyyar tunanin dan adam.
Binciken, wanda akayi ma lakabi da ‘Kiran Abinci’, wata hanya ce da mutum ke tsarawa da wani ba wai don yana kaunarshi ba sai don ya samu abincin kyauta.
KARANTA WANNAN: Yanzu-yanzu: Buhari ya samu nasarar farko, Kotun zabe ta yi watsi da bukatar Atiku da PDP na duba na'urara INEC
Binciken wanda aka gudanar akan shafukan yanar gizo, ya bayyana cewa kashi 23 zuwa 33 cikin dari na mata, na tsara wannan shiri na ‘Kiran Abinci’.
A kashin farko na binciken, an tuntubi mata 820 wanda cikinsu kashi 40 basu da aure, kashi 33 na da aure kashi 27 kuma na alaka amma basu yi aure ba. A cikinsu, kashi 85%, sun bayyana cewa suna alaka da maza, wanda hakan yasa aka gudanar da binciken a kansu.
Kusan daya bisa hudu, wanda ya kama kusan 23 cikin dari na matan da aka bincika, sun ce suna yin wannan alaka ta ‘Kiran Abinci’.
Duk da cewa wasu daga cikin mata na ganin cewa ‘Kiran Abinci’ ba wani abu bane kuma mutum zai iya yi, wasu kuma na ganin cewa bai dace ba sam.
A karo na biyu na binciken an tuntibi mata 357 da ke alaka da maza, wanda kashi 33 cikinsu suka bayyana cewa sunayin ‘Kiran Abinci’
Wanda suka gudanar da binciken sun bayyana cewa binciken nasu ba shike nuna tabbacin cewa kashin da suka samu na mata na yin wannan alakar ba. Sun kuma bayyana cewa ba wai a ko wacce alaka ake samun wannan dubarar ba sa’annan ba wai mata kadai ke yi ba maza ma nayi.
Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng