Rashin aikin yi ne ya sanya na bude asibitin qarya – Likitan bogi
-Jami'an yan sandan jihar Osun sun damke wani mutum dake gudanar da asibitin bogi a wata karamar hukuma dake jihar
-Matashin dan shekara 30 da haihuwa ya amsa cewa rashin aikin yi ne ya sanya shi fara wannan harka ta qaryar likitanci duk da cewa takardar sakandare kawai ke gare shi
Rundunar yan sandan jihar Osun sunyi nasarar damke wani Rafiu Naheem dan shekara 30 mai ikirarin likitancin qarya da kuma gudanar da asibitin bogi a karamar hukumar Odo Otin dake jihar Osun.
A wani zance da ya fito daga Adekunle Ajisebutu, jami’in hulda da jama’a na yan sandan jihar ya ce: “ Wanda ake zargin, makarantar sakandare kawai ya kammala kana kuma ya bude asibitin bogi cikin wani gida inda marasa lafiya ke yin cin-cirindo a ko da yaushe.”
KU KARANTA:Assha: Wani DPO ya kashe yarinya ‘yar shekara 16 bayan ya yi mata ciki a Katsina
Adekunle ya cigaba da cewa: “ Yayin da ake tambayar wanda ake zargin me ya sa shi yin wannan aika-aika, sai yace rashin aikin yi ne sanadi.”
Bugu da kari: “ Bincike ya tabbatar mana da cewa wannan matashi ya dade yana gudanar da asibiti cikin wani gidan da ko tsafta mai kyau bai da ita. Ya kasance yana kwantar da marasa lafiya, zubar ciki da kuma kula da matsalolin lafiya manya-manya wadanda sai kwararru ke iya duba su.”
“ Bai yi gardama bayan da ya shiga hannun hukuma, kawai abinda ya ce shi ne rashin aikin yi ne ya sanya shi fada wa cikin wannan harka. Har ila yau yace ya koyi aikin asibiti ne a wata asibiti mai zaman kanta wacce bamu san sunanta ba.” A cewar Adekunle.
Jami’in yan sandan ya kara da cewa: “ Da muke binciken gidan da yake gudanar da asibitin ta shi mun samu, abin awon jini, kayyakin awon fitsari da kuma na awon ciki da wasu kayyakin da ake amfani da su domin yin ayyuka daban-daban na asibiti.”
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng