Assha: Wani DPO ya kashe yarinya ‘yar shekara 16 bayan ya yi mata ciki a Katsina
-Idan da ranka ka sha kallo, wani jami'in yan sanda ya kashe wata 'yar aiki a Katsina bayan ya yi mata ciki
-Jami'in wanda shi ne DPO na ofishin yan sandan dake karamar hukumar Mashi ta jihar Katsina ya kashe yarinyar ne a lokacin da yake kokarin zubar mata da ciki
An samu gawar wata yarinya mai shekaru 16 da haihuwa wacce a kashe kuma aka jefar da ita cikin daji. DPO mai kula da ofishin yan sandan karamar hukumar Mashi a jihar Katsina, Garba Talawai ne ya aikata laifin kisan.
Ita dai wannan yarinyar da aka kashe, ta kasance yar aiki ne wurin budurwar DPO mai suna Safiya Danyaya.
KU KARANTA:Rundunar sojin Najeriya ta fito da sabon salon yakar ‘yan bindiga a Arewa maso yammaci
Majiyar Daily Nigerian ta tattaro rahotanni cewa, DPOn yayi kokarin zubar wa yarinyar cikin da take dauke da shi ne wanda hakan yayi sanadiyar mutuwarta.
“ A lokacin da ya lura cewa lallai ta mutu, sai ya nemi taimakon wani dan uwansa dan sanda na ya taimaka masa wurin jefar da gawar.” Inji wata majiyar da ta buqaci a boye sunanta.
Tuni Kwamishinan yan sandan Katsina, Sanusi Buba, ya sa aka kama Talawai bayan da rahotanni suka tabbatar da cewa ya aikata laifin kisan kai.
A wani zance da ya fito daga bakin mai magana da yawun hukumar yan sandan jihar Katsina, Gambo Isa ya ce: “ An samu gawar Rabi a cikin wani daji dake hanyar zuwa Mashi ranar Alhamis.”
Kakakin hukumar yan sandan ya cigaba da cewa: “ Safiya wacce ita ce budurwar Talawai ta bamu labarin cewa yar aikin ta bata ne tun ranar Laraba, kuma ta sanar da DPO kan hakan.”
A cewar Safiya“ Rabi tayi hijira ne bayan da na lura cewa tana dauke da juna biyu, wanda ya sanya na fara matsa mata.”
Isa ya tabbatar mana da cewa a yanzu haka DPO da buduwarsa na hannun ‘yan sanda domin binciken haqiqanin musabbabin kisan.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng