Jerin abubuwan 4 da suka faru cikin makon da ya gabata a siyasar Najeriya
-Abubuwa da dama sun faru a fagen siyasar Najeriya amma akwai wasu ababe 'yan kalilan da suka fi janyo hankalin jama'a inda mutane da dama su kai ta magana a kansu
-Daga cikin wadannan ababe akwai nadin mukamin shugaban kamfanin man NNPC na 19 da Shugaba Muhammadu Buhari yayi
A cikin makon da ya gabata a Najeriya, an ga abubuwa da dama da suka faru a fagen siyasa amma za’a iya cewa kalmomin da aka fi ji ba su wuce majalisa, kotu da kuma nadin mukamai ba.
Jihohin Bauchi da Kano da kuma shugabancin kamfanin man fetur na kasar nan sun mamaye duk wasu zantukan siyasa a shafukan sada zumunta da ma hirar dai-daikun mutane ta fatar baki.
KU KARANTA:Rundunar sojin Najeriya ta fito da sabon salon yakar ‘yan bindiga a Arewa maso yammaci
1. Kotun koli ta tabbatar da takarar Abba gida-gida
Ranar Talata 18 ga watan Yunin 2019 ne kotun kolin Najeriya ta tabbatar da Abba Kabir Yusuf a matsayin sahihin dan takarar gwamna karkashin jam’iyar PDP a Kano.
A baya dai, Ibrahim Al-Amin (Little) ne ya kalubalanci hallaccin takarar Abba K Yusuf kana ya maka jam’iyar PDP kotu da cewa ba’ayi zaben fidda gwamni ba. Yayi nasara a wata kotun Kano amma kotun daukaka kara ta Kaduna da kuma kotun kolin Najeriya sunyi watsi da hukuncin farkon, a karshe kotun koli ta tabbatar da Abba gida-gida a matsayin sahihin dan takarar PDP.
2. Buhari ya yi sabbin nade-nade
An wayi gari ranar Alhamis, 20 ga watan Yuni, 2019 da labarin nadin sabon shugaban kamfanin mai na NNPC a Najeriya.
Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da nadin Mele Kolo Kyari a matsayin shugaban kamfanin man NNPC na 19 wanda zai gaji Maikanti Baru yayin da zai bar aiki a watan gobe.
3. Shugaban majalisar dattawa ya fusata ‘yan APC
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Lawan ya fuskanci matsin lamba bayan da ya nada Festus Adebayo a matsayin mai ba shi shawara kan yada labarai. Mutane da dama sun riga sun san Adebayo yayi kaurin suna wurin sukar gwamnatin Buhari, bayan kwana biyu da sanar da nadin, sanatan ya sake fadin cewa ya cire shi daga mukamin.
4. An zabi kakaki biyu a majalisar dokokin Bauchi
Wata ‘yar taqaddama ta barke ranar da aka bude sabuwar majalisar dokokin jihar Bauchi, yayin da bangarori guda biyu dake hamayya da juna suka zabi shugabanni daban-daban. Yan majalisa 11 ne dake goyon bayan Gwamna Bala Muhammad na PDP suka zabi Abubakar Y. Sulaiman.
Yayin da yan majalisa guda 20 dake goyon bayan tsohon gwamna Muhammad Abubakar suka zabi Kawuwa Shehu Damina a matsayin nasu kakakin.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng