Rundunar sojin Najeriya ta fito da sabon salon yakar ‘yan bindiga a Arewa maso yammaci

Rundunar sojin Najeriya ta fito da sabon salon yakar ‘yan bindiga a Arewa maso yammaci

-Rundunar sojin kasan Najeriya zata sanya hanyoyin zamani wurin yakar 'yan bindiga a yankin Arewa maso yammacin kasar

-Babban kwamandan runduna ta 8 mai kula da jihohin Sokoto, Kebbi, Zamfara da Katsina ne ya bada wannan bayani yayin da ya kai ziyara fadar gwamnatin jihar Katsina ranar Alhamis

Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce ta fitar da sabbin hanyoyin murkushe ‘yan bindiga a yankin Arewa maso yammacin Najeriya ciki hadda na’urar daukan hotunan sirri wacce aka fi sani da duron.

Babban kwamandan rundunar sojin kasa ta 8 dake Sokoto, Birigediya Janar Abdulkarim Oladapo Okiti ne ya bayyana wannan labarin jiya Alhamis a Katsina yayin da ya kai ma gwamnan jihar Aminu Masari ziyara.

KU KARANTA:APC tayi watsi da zaben Kakakin Majalisar Bauchi, ta zargi magatakardan majalisar da aikata rashin gaskiya

Kwamandan ya ce: “ Wannan ziyarar ta wa nada nasaba da umarnin shugaban kasa kan cewa lallai mu tashi tsaye domin ganin mun murkushe ayyukan ‘yan bindigan a wannan yankin.”

A cewar Okiti: “Rundunar da nake jagoranta na lura ne da jihohin Sokoto, Kebbi, Zamfara da Katsina. Kari a kan na’urar daukan hotunan sirri ta duron akwai wasu tsare-tsare na daban da muka sauya domin kawo karshen ta’addancin ‘yan bindiga.”

Bugu da kari, kwamandan ya ce, yin amfani da zamani ya zama wajibi saboda yin badda kama ga ‘yan ta’addan.

Kwamandan ya cigaba da cewa: “ Shigo da zamani da mukayi cikin yakin idan aka hada da jajircewar jami’anmu ko shakka babu muna daf da ganin bayan ‘yan taddan.”

Haka zalika, Okiti ya sake cewa, “dadin dadawa a cikin sabon tsarin yakar ‘yan bindigan an tura da dakaru gonaki da kuma kasuwannin kauye domin samar da kariya ga manoma da kuma masu zuwa cin kasuwa.”

Da yake na shi jawabin, Masari cewa yayi: “ Mazauna yankunan dake cikin dar-dar na barazanar ‘yan bindigan zasu ba jami’an sojin goyon baya wurin gudanar da aikin nasu ta hanyar sanar da su duk wani bayani da kan taimaka masu wurin murkushe ta’addancin.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng