Matar gwamnan Bauchi ta gudanar da gangamin duba lafiyar mutane 1000 kyauta
-Uwar gidan gwamnan Bauchi hadaka da bankin Fidelity, sun dauki nauyin duba lafiyar mutane 1000 a karamar hukumar Misau dake jihar Bauchi
-Matar gwamnan ta kara da cewa harkar kiwon lafiya na daya daga cikin mahimman abubuwa da gwamnatinsu zata sa a gaba
-Haka zalika ta yi kira ga wadanda suka mafana da shirin da su yawaita ziyartar asibitoci don duba lafiyarsu
Matar gwamnan Bauchi Hajiya Aisha Bala Muhammad ta gudanar gangamin duba lafiyar mutane 1000 kyauta, a karamar hukumar misau a jihar Bauchi.
Gidauniyar uwar gidan gwamnan Al-Muhibbah da bankin Fidelity ne suka shirya gangamin. A lokacin da take jawabi ga wadanda suka amfana da shirin, Hajiya Aisha ta yi kira garesu da su rinka yawan duba lafiyarsu dan su san matsayarsu wanda hakan zai rage hadarin kamuwa da cutar sikari, ciwan daji, hawan jini da dai sauran cututtuka.
KARANTA WANNAN: Garuruwa biyar da mata ke auren fiye da namiji guda
Ta kara da cewa rashin samun isasshen abinci da rashin asibitoci da wajajen kiwon lafiya na daya daga cikin matsalolin da ake da bukatar a magance a jihar.
Ta kara da cewa harkar lafiya na daya daga cikin abubuwa masu mahimmaci da gwamnatinsu zata duba a jihar, saboda haka ta bukacesu da su cigaba da yima saban gwamnan addu’a don ganin ya cika alkawurran da yayi a lokacin da yake kamfen.
Matar gwamnan ta kara da cewa gidauniyar ta, Al-Muhibbah na da zummar taimakawa mata da kananan yara ta fannin kiwon lafiya da harkar ilimi.
Uwar gidan gwamnan, ta yaba da kokarin bankin Fidelity da ya taimaka wajen ganin an gudanar da gangamin.
Ta godema sarkin Misau da ya sanya aka tattara mutanen da suka mafana da shirin, da kuma irin shawarwarin da yake basu akan harkar lafiya.
Wadanda suka amfana da gangamin na gidauniyar Al-Muhibbah da bankin Fidelity, sun gode masu da suka zabi Misau a matsayin wajen da zasu gudanar da taimakon.
Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng