Garuruwa biyar da mata ke auren fiye da namiji guda
-A wasu kasashe, mata na da damar su auri mazaje da yawa kuma su zauna dasu zaman aure a lokaci guda
-Wasu addinai da al'adunsu sun karfafa su rinka yin wannan aure
-Idan macen ta haihu, to sai a baiwa namijin da take gidanshi a lokacin dan da ta haifa, a wasu wuraren kuma, dan da ta haifan zai samu uba fiye da daya
Ba sabon abu bane a ce namiji ya auri mace fiye da daya, wasu al’adun da addinai ma sun karfafa hakan. Amma abun mamaki ne aji cewa mace ta auri fiye da namiji guda tana zama dasu a lokaci daya.
Shi de wannen wani irin aure ne da mace ke auren maza biyu ko sama da haka a lokaci guda. Alal misali, yan Tibetans da ke a Nepal, wadda tayi boda da China da kuma Arewacin India, maza yan gida biyu na iya auren mace guda su zauna da ita a lokaci guda kuma ta rinka raba kwana a tsakaninsu dai-dai wa daida.
KARANTA WANNAN: Muna da takardun da za mu kama Dankwambo a hannunmu – Gwamnatin Gombe
Anan zaka ga wasu kasashe biyar da kabilun da suke yin irin wannan aure:
Najeriya
Duk da de cewa mafi yawan yan Najeriya basu yin irin wannan auren, amma akwai kabilar da take yin irinshi. A kabilar Irgwe dake a arewacin Najeriya, mata na iya auren fiye da namiji guda. Yan kabilar suna yin irin wannan auren da jimawa har sai a shekarar 1968 lokacin da yan majalisar su suka canza wannan tsarin, aka haramta irin wannan auren.
Kafin nan, macen zata rarraba kwanan a tsakanin mazajen kuma idan ta samu ciki to sai a baiwa wanda take a gidansa a lokacin.
Indiya
Indiya na da kabila fiye da daya dake irin wannan auren. Auren yafi yawa ne a fadin arewacin Indiya inda yan kabilar Paharis da Kinnaru ke yinshi.A matsayinsu na tsatson Pachi Pandavas, (inda maza biyar yan gida guda suka auri wata yarinya mai suna Draupadi yar sarkin Panchala) suna gani cewa tilas ne su dabbaka al’adarsu.
A wani bincike da jami’ar Tibet tayi, an gano cewa a shekarar 1988, kasi 13% na ahalin Tibet na yin irin wannen auren.
Kenya
A cikin watan Agusta na shekarar 2013, an gudanar da irin wannan aure a Kenya, bayan da wasu maza guda biyu suka yanke shawarar auren mace guda. Abin lura anan shine dokokin Kenya basu haramta yin hakan ba, a sabida haka ba za a iya kaisu kara ba. Akwai kuma rahotannin cewa yan kabilar Masai na kasar ta kenya na yin irin wannan auren.
China
A China ana yin irin wannan aure a kabilar Tibet dake a Nepal, su a can, yaro yana iya samun fiye da mahaifi daya. Kuma idan yan gida guda suka auri mace to dukkansu zasu zauna da ita a matsayin matarsu a lokaci guda. Ana yin irin wannan auren ne musamman idan iyalin basu da hali sosai, a sabida haka sai su auri mace guda ta yadda yayansu zasu zama daya su cigaba da kula da yar karamar gonarsu.
America ta Kudu
A Amurika a kudu. A kabilar Bororo, mace zata iya auren fiye da namiji guda. Haka zalika kashi 70% na yan kabilar Tupi Kawahib na yin irin wannan auren
Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng