Dankari: Dan wasan kwallan kafa na Najeriya ya siya ma matarshi dankareriyar mota

Dankari: Dan wasan kwallan kafa na Najeriya ya siya ma matarshi dankareriyar mota

-Winfred Ndidi, dan wasan kwallan kafa na Najeriya ya siya ma matarshi sabuwar mota G-Wagon wata daya bayan aurensu

-Dan wasan kwallan kafar da ke buga ma kungiyar Liecester City, a halin yanzu yana Misira tare da sauran yan wasan kwallan kafa na Najeriya suna shirin gasar cin kofi na Afirika.

-Ndidi da abokan wasan shi zasu fuskanci kasar Burundi a ranar Asabar 22 ga watan Yuni 2019.

Dan wasan tsakiya na kwallan kafa ta super Eagles ya nuna alamun kulawa da kowane namiji ya kamata ya nuna ma matarshi. Dan wasan ya siyawa matarshi mai suna Fortune sabuwar mota kirar G-wagon don tayata murnar bikin ranar haihuwarta.

KARANTA WANNAN: Hukumar NAFDAC ta haramta sayar da fiya fiyan 'Sniper' a kasuwann

Kwanannan Ndidi ya auri Fortune bayan da suka jima suna soyayya. Bikin ya samu halartar manyan shuwagabanin gudanarwa ta kwallan kafa ta Najeriya, yan uwa da abokan arziki, da abokin wasansa na Liecester City Kelechi Iheanacho.

An ta tsammanin cewa Ndidi da matar tasa zasu zagaye duniya don su ci amarcinsu amma aikin wasan kwallan kafa ta Najeriya ya kawo ma sa cikas.

A yanzu haka yana Misira da saran yan wasa kwallo ta Super Eagles suna shirye shiryen buga wasan su na farko da kasar Burundi a gasar cin kofin Afirika.

Ana hakan ne wani hotan bidiyo ya watsu a yanar gizo inda aka ga ana mika ma matar Ndidi kyautar G-wagon a yayinda ita kuma take cike da murna.

An daura auren Ndidi da Favour a ranar Asabar 25 ga watan Mayu 2019 a wata choci a babban birnin Najeriya Abuja.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng