Jami’ar Ghana ta kori Farfesan Najeriya bayan da ya ci mutuncin kasarsu
-Jami'ar horar da malamai ta Ghana dake Wninneba ta kori wani Farfesan Najeriya kan kalaman batanci da yayi wa kasar
-Farfesan wanda yake aiki tare da jami'ar tun watan Oktoban 2018 yayi abinda ya fusata jami'ar yayin da su kuwa ba suyi jinkiri ba wurin sallamarsa
Jami’ar horar da malamai ta Winneba a kasar Ghana ta sallami farfesa dan kasar Najeriya mai suna Farfesa Augustine Uzoma Nwagbara.
Jami’ar ta kori Mista Uzoma ne bisa dalilin bata sunan kasarsu da yayi cikin wani bidiyo da ya riga ya karade shafukan sada zumunta a halin yanxu.
KU KARANTA:Lawan Ahmad ya nada hadimai 3 wadanda su kayi aiki da Saraki
A shafin yanar gizo na jami’ar, an rubuta kadan daga cikin abinda Farfesan ya aikata musamman saboda kowa ya san dalilin da yasa jami’ar ta sallame shi.
Ga binda zancen ke cewa: “ An sallami Farfesa Augustine Uzoma Nwagbara daga jami’ar horar da malamai ta Ghana, “ Hukumar gudanarwar jami’ar na sanar da jama’a cewa ta dauki wannan matakin ne bisa wani bidiyo dake yawo a shakufan sada zumunta inda Farfesa Uzoma yayi kalaman batancin ga kasarmu.”
“ Augustine Uzoma Nwagbara, Farfesa ne wanda ya kware a fannin harshen turanci. Ya kuma kasance a nan tare da jami’armu tun watan Oktoban 2018.”
“ A cikin bidiyon, Farfesa yayi maganganu marasa dadi game da tarihin kasarmu da kuma tsarin bayar da iliminta. Wannan abu ko kadan bai yi mana dadi ba.”
“A dalilin haka ne jami’armu ke amfani da wannan kafar domin sanar da ilahirin jama’ar Ghana cewa ko kadan bata goyon bayan kalaman Farfesan kuma tayi tir da kalaman nasa gaban dayansu.”
“ Ba Uzoma bane dan Najeriya na farko da ya fara zuwa jami’ar nan tamu ba domin koyarwa. Wasu da yawa sun zo gabaninsa, sai dai ba su aikata irin wannan laifin nasa ba. Bayan bincike da kwamitin da jami’a ta kafa kan wannan bidiyo an sa ma Farfesa da laifi a don haka mun kore shi.” Kamar yadda zancen ya bayyana mana.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng