Wata yarinya taji dadin Dubai ta rusa ma iyayenta kuka cewa bazata dawo Najeriya ba
-Wata yar karamar yarinya mai suna Anjola, tayi bikin ranar haihuwarta na biyar a Dubai
-Amma bayan an gama shagalin bikin, sai yarinyar da mahaifiyarta suka dawo najeriya
-Anjola de ta cije a bakin kofar gidansu tana rusa kuka cewa bazata shiga ba saboda babu wuta
Najeriya wata kasa ce mai cike da abin al’ajabi. Mutanen kasar sun saba da yanayin da kasar take kuma suna jin dadin rayuwarsu a cikinta. Amma ga alamu wadanda ke jin dadin zamansu a kasar, basu taba jin dadin da yafi wanda suke ciki ba.
Wani bidiyo ya watsu a kafafen sada zumunta na wata yarinya da ta ki shiga gidansu bayan da suka dawo daga Dubai tare da mahaifiyarta.
Anjola ta yi bikin murnar cika shekara 5 a Dubai kuma ga alama ta ji dadin zuwanta kasar. Hakan ya bayyana ne bayan da ta ki shiga gidansu bayan sun dawo tare da mahaifiyarta.
KARANTA WANNAN: Hukumar NAFDAC ta haramta sayar da fiya fiyan 'Sniper' a kasuwanni
A bidiyon anga yarinyar na ta rusa kuka tana cewa ita bazata shiga gidan ba saboda babu wuta. An kuma ji muryar mahaifiyar ta ta tana rokonta da tayi hakuri ta shigo.
Anjola dai ta shiga gidan bayan da mahaifiyar tayi mata alkawarin zasu koma dubai bayan ta share kusan minti 40 tana rokonta.
A wani labari makamancin wannan, kwanan baya da suka wuce legit.ng tayi hira da wata yarinya da ake tsammanin tafi kowa kyawu a duniya.
A cikin shekarar 2018 ne, iyalan yarinyar masu karamin hali, suka tashi da labarin wanda hakan ne ya chanza masu rayuwarsu har abada kuma soyayyarsu ta shiga zukatan al'umma bayana da hirar ta watsu a duk fadin duniya ta hanyar yanar gizo.
Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng