Amfanin su Buratai ya riga ya kare, wata jam’iyar siyasa ta fada wa Buhari

Amfanin su Buratai ya riga ya kare, wata jam’iyar siyasa ta fada wa Buhari

-Yabagi Sani ya bai wa shugaban kasa shawara kan yadda za'a magance matsalolin tsaron kasar nan

-Yabagi wanda shi ne shugaban jam'iyar Action Democratic Party (ADP) ta kasa ya koka kan barin hafsoshin jami'an sojin Najeriya su wuce lokacin da ya kamata a ce sunyi murabus da cewar shi ne ya haifar da wannan matsala

Shugaban jam’iyar Action Democratic Party (ADP), Yabagi Sani ya ce: “ Kalaman da Buratai yayi na cewa dakarun sojin Najeriya a yanzu ba su bin umarninsa tamkar ya gogawa kansa ne da Shugaba Buhari kashin kaji.”

Ya cigaba da cewa: “ Mukaman shugabanni tsaro yakamata a ce an sauya su tun ba yau ba saboda wa’adinsu ya cika. Amma jam’iyar APC ta ki yin wani abu a kai inda aka bar su kan mukaman na su duk da cewa lokacinsu na yin murabus ya yi.”

KU KARANTA:Oyegun: APC zata iya faduwa zaben gwamnan Edo na shekara mai zuwa

Bugu da kari shugaban ADP ya sake cewa: “ Ta yaya za’a samu jajircewa da bin umarni daga wurin dakarun bayan an barsu babu wadatattun kayan aiki. Ko haqqinsu ma ba samu suke ba, kuma wannan duk ya ta’allaka ne a kan halin ko oho da shugaban kasa yake nuna wa wurin sauyan hafsosin sojin.”

“ Abin na da daure kai, idan ka lura cewa rashin tsaro wadanda ake kuka da shi tun lokacin gwamnatin da ta gabata yanzu abin kara lalacewa yayi maimakon a ce an samu sauki. Ga shi kuma wanda ke mulki a yau tsohon janar ne mai ritaya.” A cewar Yabagi.

“ Hafsun sojin kasa na Najeriya, ya riga da ya nuna gazawarsa cikin kalamansa, inda yake cewa yanzu dakarun na sa ba suyi masa da’a kan umarnin da yayi masu. Yanzu aiki ya rage kan Shugaba Buhari na ya sauke ilahirin hafsoshin domin sanya wasu jajirtattun.” Kamar yadda ya shaidawa jaridar The Nation.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng