Mutanen kirki basu karewa: Wani direba ya nuna dabi’arsa ta kwarai

Mutanen kirki basu karewa: Wani direba ya nuna dabi’arsa ta kwarai

-Wani direban tasi ya kara tabbatar da cewa lallai har yanzu akwai mutanen kirki acikin al’umma.

-Direban ya mayar ma wata fasinja sabuwar wayarta kirar Iphone 7 plus da ta manta a motarsa

-Alex ya kuma bayyana cewa shi mutumen kirki ne, kuma ya sha mayarwa da fasinjoji kayansu da suka manta a motarsa

Alex Boakye, wani direban tasi dake tuka mota kirar Toyota Corolla mai lamaba GX-3151-14, yayi wani abinda mafi yawan direbobin tasi na Accra da sauran fadin duniya ba za su yi ba, bayan da ya mayarwa wata mata mai suna Ewurabe sabuwar wayarta kirar Iphone 7 plus da ta fadi a cikin motarsa a ranar Litinin 17 ga watan Yuni 2019.

Bayan da aka kira wayar, Alex ya daga, ya kuma yima mai wayar alkawarin zai mayar mata da wayarta kuma ya bata lambar wayarsa don ya kara tabbatar mata da cewa zai maido mata.

KARANTA WANNAN: Rikicin raban gadon Marigayi sanata Usman Albashir

Ewuraben, mai wayar, ta bada labarin abinda ya faru kamar haka “An kira wayar kuma ya amasa, sa’annan ya bamu lambar wayarsa. A lokacin yana Nsawam saboda haka sai cikin dare ya kawo wayar.”

Alex ya bayyana cewa bai taba ajiye kayan fasinja ba a motarsa tun sadda ya fara tuki.

“Banga dalilin da zai sa in ki maida kayan da aka manta a motata ba. Ko satin da ya wuce, wata mata ta manta wayarta, saida nayi tafiya mai nisa na maida mata. Ni mutum ne mai amana saboda ina da ya’ya kuma akwai bukatar in koya masu dabi’u na gari.”

Ya ba sauran yan tasi shawara su kwaikwaiyi irin dabi’unsa saboda a rinka girmama sana’ar tasu.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng