Hukumar NAFDAC ta haramta sayar da fiya fiyan 'Sniper' a kasuwanni
-Hukumar NAFDAC ta hana sayar da maganin fiya fiyan 'sniper' a kasuwanni da manyan shaguna
-Darakta a hukumar, Dr. Bukar Usman ne ya bayyana hakan. Ya ce hukuncin ya biyo bayan yadda mutane ke amfani da maganin suna halaka kansu
-Daraktan ya bayyana cewa ba wai za a hana sayar da maganin bane baki daya, illa de za a rinka sayar da shi ga manoma ne kawai
Hukumar kula da ababen ci da sha da magunguna (NAFDAC) ta umurci dilolin magungunan aikin gona da zu janye fiya fiyan 'Sniper' daga kasuwannin game gari da kuma manyan shaguna, sakamakon yadda mutane ke amfani da maganin suna kashe kansu a yan kwanakinnan.
Daraktan hukumar, Dr.Bukar Usman ya bayyana hakan a ranar Laraba 19 ga watan Yuni 2019 a makarantar aikin gona dake Ibadan.
A lokacin da yake magana wajen bikin kaddamar da wani maganin beraye ga manoman rogo mai suna “Lifeline”, Usman ya ce hukumar ta umurci dilolin magungunan aikin gona da su daina siyar da fiya fiyan 'Sniper' a kasuwannin game gari da manyan shaguna.
KARANTA WANNAN: Akwai bukatar a binciki Gwamnatin Misra wajen mutuwar Morsi - Erdogan
A cewarshi, fiya fiyan 'Sniper' magani ne da akayishi domin aikin gona kawai ba don kashe kwarin cikin gida ba.
Ya bukaci masu hada maganin da diloli da su ba hukumar hadin kai don ganin an tsayar da sayar da maganin da ke a ko ina barjat.
Ya kara da cewa ba wai an dakatar da sayar da maganin bane baki daya, illa de za a takaita siyardashi ga manoma kawai, ya kuma kara da cewa duk magungunan aikin gona bai kamata a rinka kaisu gida ba, a rinka barinsu a gona kawai.
Ya ce “Akawai magungunan sauro da kwarin cikin gida ingantattu.” Ba wai lallai dole sai anyi amfani da maganin fiya fiyan 'Sniper ba' ba.
Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng