Da gaske ne mata sunfi maza yawa a duniya? Ga amsar cikin wannan labari

Da gaske ne mata sunfi maza yawa a duniya? Ga amsar cikin wannan labari

-An dade ana tsammanin cewa mata ne suka fi maza yawa a yau bisa la'akari da yawan al'ummar duniya a yanzu

-Sai dai kash, lissafi ya sha bambam yayin da Majalisar Dinkin duniya ta fitar da wata kididdiga wacce ke nuna yawan al'ummar dake duniya da kuma yawan ko wane jinsi

Ba mamaki idan ka ji ana tambaya tsakanin maza da mata wadanne suka fi yawa, wucewa za ka yi abinka, ba sai ka tsaya bayar da amsa ba bisa tunanin cewa mata ne mafiya yawa.

Wata kila saboda matan da suka taru a gidanku a biki na karshe da aka yi a gidan ko kuma a makobta suna da yawan da ya zarce kirge, ko kuma matan dake gidanku sun dara mazan yawa.

KU KARANTA:Yanzu Yanzu: An sako dan ministan Buhari da masu garkuwa da mutane suka sace

Kai a matsayinka na saurayi kana da ‘yan mata sun kai biyar, ke kuma budurwa kila samarinki sun fi goma, a don haka kowa na gina tunaninsa a kan tsammani.

Ko ma dai mene ne, wani rahoton Majlisar Dinkin duniya ne ya bayyana cewa yawan mutanen duniya ya kai biliyan 7.7 inda ya bayyana cewa maza sun dara mata yawa.

Rahoton ya bayyana cewa Najeriya na da yawan mutane miliyan 200 da ‘yan kai, inda yawan maza ya kai miliyan 101 na mata kuma miliyan 99.

Hakan na nuna cewa maza sun dara mata yawa da tazarar kimanin miliyan 2.7 a Najeriya. Su kuwa masana cewa suke nan da shekarar 2040 yawan mutanen kasar zai ninka har sau uku, ba kuma tare da wasu kayayyakin more rayuwa ba.

Wannan rahoto ya ci karo da imanin mutane da dama, don haka ne ma shafin BBCHausa na sada zumunta ya samu jin ta bakin mutane inda kowa ya bayyana nasa ra’ayin da kuma amsoshi kan wannan tambaya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng