Neymar zai bar kungiyar PSG

Neymar zai bar kungiyar PSG

-Alamu na nuna cewa babu tabbaci Neymar zai cigaba da zama a kungiyar zakarun gasar kwallan Faransa PSG

-Dan wasan dan asalin kasar Biraziliya ya gayama shuwagabannin kungiyar cewa yana so ya bar kungiyar

-Zakarun kwallan kafa ta kasar Sifaniya, Barcelona na so ta sake siyan dan wasan gaban

Neymar ya bayyana ma shuwagabannin PSG cewa ya naso “ya koma gida” bayan da ya ce yayi kuskuren barin kungiyar Barcelona.

Dan kwallan kafar wanda dan asalin kasar braziliya ne ya bar kungiyar kwallan kafa ta Barcelo zuwa kungiyar PSG a cikin shekarar 2017 akan kudi Euro miliyan 198.

Amma rahotanni da ke fitowa daga kasar Sifaniya na nuna cewa Neymar ya bayyanama kungiyar PSG cewa cigabanshi bai ta’allaka da kungiyar ba.

A rahoton jaridar Daily Mail, manajan na PSG Mundo Deportivo ya ce ya gaji da matsalolin Neymar ne ba wai don Neymar din na so ya tafi ba.

KARANTA WANNAN: Abinda yasa mu ka goyi bayan Aisha Buhari a kan batun 'First lady' - APC

Neymar ya bayyana ma Mai kungiyar ta PSG Nasser Alkhelaifi cewa “Bani so in sake buga ma PSG. Ina so in koma gidana inda bai kamata in baro ba tun farko

Bugu da kari El Mundo ya bayyana cewa kungiyar ta Barcelona na so ta karkata akalar yarjejeniyar da takeyi da kungiyar Atletico Madrid game da dan kwallan Atletico Griezmann, kai tsaye zuwa PSG don ganin ta mallaki Neymar.

Neymar da mai kungiyar ta PSG Alkhelaifi na samun matsala a yan kwanakin nan. Alkhelaifi ya nuna bacin ransa game da Neymar a wata fira da akayi dashi satin da ya gabata.

A wata hira da France Football Alkhelaifi ya bayyana cewa “Ina son yan wasa da zasuyi duk abinda zasuyi don su kare mutuncin rigarmu.”

Hakan ya biyo bayan yan wasannin

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng