Mutane masu hazaka yakamata a sa matsayin ministoci – Wata jam'iyyar siyasa ta fada wa Buhari

Mutane masu hazaka yakamata a sa matsayin ministoci – Wata jam'iyyar siyasa ta fada wa Buhari

-Shugaban wata jam'iyar siyasa ya ba Buhari shawara kan irin nau'in mutanen da ya kamata a ce ya nada matsayin ministocinsa

-Wannan shawarar ta biyo bayan taron kwamitin zartarwar jam'iyar ZLP wanda akayi ranar Talata a Abuja, inda shugaban ke cewa yanzu yan Najeriya ba su iya hakurin wata shida babu ministoci

Shugaban jam’iyar Zenith Labour Party (ZLP), Cif Dan Nwanyanwu ya bai wa Shugaba Buhari shawara kan irin mutanen da ya dace ya zaba matsayin ministoci a wa’adinsa na biyu.

Nwanyanwu ya yi wannan kalamin jiya Talata a Abuja yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan kammala taron kwamitin zartarwar jam’iyar tasu.

KU KARANTA:Yanzu-yanzu: Gobara ta barke a babbar kasuwar Binuwe

Shugaban jam’iyar ya ce: “ Yan Najeriya basu iya jiran tsawon wata shida a yanzu ba tare da an nada ministoci ba, wadanda zasu kula da ma’aikatu daban-daban na kasar nan, kuma ya kasance an zabi jajirtattu masu hazaka.”

“ A halin yanzu kamata yayi a ce shugaban kasa ya aika da sunaye majalisar dattawa domin tantancewa. Ba za mu iya jira ba gaskiya. Babu dan Najeriyar da zai yi hakurin jira kamar yadda mu kayi a zango na farko. Kamar yadda ya ce ya fahimci kura-kuransa kamata yayi mu ga canji tun yanzu.

“ Ina da yaqinin cewa ba zai barmu muna jira ba. A don haka yan Najeriya na nan sun zuba ido su na son ganin sunayen ministoci ya isa majalisar dattawa kafin karshen watan Yuni.” Inji Nwanyanwu.

“ Yanzu duk wani korafi ya riga da ya kau, saboda ba ma zamu karbi ko guda ba. majalisar dokokin tarayya a yau na karkashin kulawar shugaban kasa ne, a don haka yan Najeriya aiki kawai suke jira ba tare da wani korafi ba kamar yadda akayi a baya.” A cewar shugaban ZLP.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng