Ajali in yayi kira: Wani birkila ya yiwa karuwarshi mari daya tal, ta sheka lahira

Ajali in yayi kira: Wani birkila ya yiwa karuwarshi mari daya tal, ta sheka lahira

- An kama wani birkila ya kashe wata karuwa a Otel a garin Ilorin

- Rahotanni sun bayyana cewa birkilan ya mari karuwar ne, bayan sun yi yarjejeniya akan kudin da zai bata ya kasa cikawa

- Yanzu haka dai kotu ta sa a tsare shi a gidan kurkuku har sai lokacin da aka kammala shari'arsa

Ranar Litinin dinnan ne wata kotu dake garin Ilorin babban birnin jihar Kwara ta yankewa wani birkila mai suna Sodiq Kazeem hukuncin dauri a gidan yari bayan ta kama shi da laifin kashe wata karuwarshi a Otel.

Alkalin kotun Mai Shari'a Mary Bamidele ta bada umarnin cewar a daure Kazeem a gidan yarin Mandala dake cikin birnin Ilorin har zuwa lokacin da za a kammala shari'ar shi.

Kotun ta ce za ta cigaba da sauraron karar ranar 28 ga watan Yuni.

Lauyar da ta shigar da karar mai suna Rodah Kayode ta bayyanawa kotu cewa Kazeem ya aikata laifin nasa ne a ranar 30 ga watan Mayun da ya gabata.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Shaidan ne ke hada Sarkin Kano da Ganduje rigima - Attahiru Bafarawa

Roda ta bayyana cewa jami'an tsaro ne suka cafke Kazeem bayan ya kashe karuwar mai suna Yemisi Adekoya a Otel din da ke Coca-Cola dauke da fankar Otel din da ya sato.

"Binciken da aka gabatar ya nuna cewa fada ne ya shiga tsakanin Kazeem da Yemisi akan kin biyanta haqqinta da yayi bayan sun gama holewa.

"Kazeem ya bayyana cewa sunyi ciniki da karuwar akan zai ba ta naira 2,500, sai kuma aka samu matsala, bayan sun gama sai ya bayyana mata cewa kudin dake wurinsa ba su kai yadda suka yi ciniki ba.

"Yemisi ta mare shi a take a wajen ganin cewa kudin da ya bata bai cika ba, sai shi ma fushi ya dibeshi ya juya ya gaura mata mari. Marin ta ke da wuya ashe yayi marin akan gaba ne domin kuwa ajali yayi kira, nan take ta fadi ta ce ga garinku nan."

Sai dai kuma shi Kazeem ya musanta hakan a gaban kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel