Yanayin kasa: Ka saurari shawarar Obasanjo, kungiyar Fulani ta fada wa Buhari

Yanayin kasa: Ka saurari shawarar Obasanjo, kungiyar Fulani ta fada wa Buhari

-Alhaji Sale Bayari ya roki gwamnatin Shugaba Buhari kan sauraron shawarwari daga wurin tsoffin shugabannin Najeriya da kuma wasu manyan mutane dake da kishin kasar Najeriya.

-Shugaban kungiyar Gan Allah ta cigaban Fulanin Najeriya ya ce, idan gwamnati ta kasance ta na amfani da abinda Obasanjo ke bada shawara a kai to tabbas za'a samu cigaban da ake nema, saboda shi mutum ne mai hangen nesa.

Kungiyar Gan Allah ta cigaban Fulanin Najeriya ta shawarci Shugaba Buhari da ya saurari shawarwarin Obasanjo kan harkokin da suka shafi Najeriya.

Alhaji Sale Bayari, shugaban kungiyar na kasa ne yayi wannan kira yayin wata zantawa da manema labarai jiya Litinin a Jos dake jihar Filato.

KU KARANTA:A karo na biyu, gwamnatin jihar Taraba ta kara saka dokar hana fita a Jalingo

A cewarsa: “ Obasanjo ya san matsalar Najeriya, idan har gwamnati za ta saurare shi to babu shakka matsalar Najeriya ta kau.”

“ Domin ciyar da kasar nan gaba, ya zama wajibi ga gwamnati ta saurarin shawarar tsoffin shugabanni ba tare da duban jam’iyar da suka fito ba. Tsohon shugaba Olusegun Obasanjo na daya daga cikinsu. Da ace wata kasa a Africa zatayi amfani da ilimin Obasanjo na sanin mulki da an samu canji gaskiya.

“ Ko shakka babu, Obasanjo mutum ne mai ilimi da kuma kwarewa kan sanin Najeriya musamman a fanni mulki. Babu wani mahaluki a yau dake a raye ko a mace da yake tunani tamkar yadda Obasanjo ke yi. Ya san Najeriya ciki da waje, nahiyar Afrika da ma sauran kasashen duniya tamkar bayan hannunsa.”

“ Mun sani cewa gwamnati za ta iya sa wa ayi ko a bari, amma shawarwarin tsoffin shugabanni wadanda suke manya a kasa na da matukar amfani. Akwai manya mutanen da ya kamata ace gwamnati na neman shawararsu kamar su: Yakubu Gowon, Ango Abdullahi, Sarki Muslumi, Sarkin Ife da dai sauransu.” Inji Bayari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng