Rai bakon duniya: Wani matashi ya mutu cikin tafki a Kano

Rai bakon duniya: Wani matashi ya mutu cikin tafki a Kano

-Wani matashi mai shekaru 20 ya mutu cikin tafki yayin da yaje domin yin wanka.

-Rahotanni sun nuna cewa matashin dan shekaru 20 da haihuwa mai suna Mustapha Abdullahi ya mutu a cikin tafkin bayan da ruwa ya ja shi har ya nutse ciki.

-Hukumar 'yan kwana-kwanan jihar Kano sun yi iya bakin kokarinsu domin ceto rayuwar wannan bawan Allah sai dai abin ya ci tura, kamar yadda jami'in hulda jama'a na hukumar ya bayyana ma kamfanin dillacin labarai na kasa wato NAN.

Mustapha Abdullahi, mai shekaru 20 da haihuwa ya gamu da ajalinsa yayin da yake wanka cikin tafkin dake shiyar Kofar Mata a Kano.

Saidu Muhammad, jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan kwana-kwanan jihar Kano ne ya bada wannan labari ga kamfanin dillacin labaran Najeriya a ranar Juma’a.

KU KARANTA:Rashawa: Kotu ta dage sauraron karar Jonah Jang har zuwa 27 ga watan Yuni

Muhammad ya ce: “ Wannan al’amari ya auku ne a safiyar Juma’a yayin da mamacin ya tafi tafkin domin yin wanka.”

“ A safiyar juma’a ne da misalin karfe 8:00 muka samu kiran waya daga wani Mallam Rabiu ya ce mana an ga Abdullahi kwance a kan ruwa.

“ Bayan mun samu wannan kira, sai mu ka aika da tawagar jami’ai domin ganin ko za’a iya ceto rayuwarsa da misalin karfe 8:06.”

“ Ko da jami’anmu suka tsamo shi daga cikin ruwan, bai san inda kansa yake ba, a nan aka garzaya dashi asibitin kwararru ta Murtala Muhammad inda aka tabbatar da mutuwarsa.” A cewar jami’in.

A halin yanzu dai ba’a san menene musabbabin mutuwar wannan matashi ba. Muhammad yayi kira ga iyaye da kuma masu unguwanni dasu rika hana yara zuwa yin wanka a irin wadannan wurare. (NAN)

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel