Ya kamata a samar da dokar yaye bambanci tsakanin Mata da Maza a fagen aiki - Dangote

Ya kamata a samar da dokar yaye bambanci tsakanin Mata da Maza a fagen aiki - Dangote

Mutumin da ya fi kowa dukumar dukiya da kuma tarin arziki a nahiyyar Afirka Alhaji Aliko Dangote, ya shawarci gwamnatin Najeriya da kuma dukkanin masu ruwa da tsaki a kan yaye bambanci tsakanin Mata da Maza a fagen aiki.

Fitaccen attajirin ya nemi da yaye shamaki na nuna bambance bambance tsakanin Mata da Maza domin inganta harkokin gudanar da zai bunkasa ci gaban kasar nan.

Cikin jawaban da ya gabatar a taron manyan Mata masu rike da madafan iko a ma'aikatun gwamnati da kuma na masu zaman kansu, Dangote ya nemi da a kwantanta daidaito a tsakanin Mata da Maza a wuraren aiki.

Ya bayar da misalin bai wa Mata dama ta kaso 30 cikin dari yayin da Maza ke da kaso 70, Dangote ya ce ci gaba da karuwar adadin Mata a masu rike da madafan iko a wuraren aiki na da tasirin gaske wajen samar da sabbin tsare tsare dake bunkasa harkokin gudanarwa a kasar nan.

KARANTA KUMA: Tilas na koma majalisar Buhari - Dalung

Kasancewar sa fitaccen dan kasuwa, Dangote ya hikaito yadda 'ya'yan sa Mata uku da sauran Mata ke rike da madafan iko a masana'antun sa daban daban inda a cewar sa kowacce na ci gaba da nuna bajintar gaske ta samar da nasarori marasa iyaka.

Cikin wani rahoton mai nasaba da jaridar Legit.ng ta ruwaito, Dangote ya ce Najeriya ba za taba kai wa tudun mun tsira ba ta fuskar samun ci gaba muddin wutar lantarki ba ta wadata ba tamkar sauran kasashe da ke daga yatsa na bunkasar tattalin arziki.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel