Gwamnan Zamfara ya dakatar da Sarki da Hakimi

Gwamnan Zamfara ya dakatar da Sarki da Hakimi

Gwamnan jihar Zamfara, Dr. Bello Muhammad Mutawalle, ya amince da dakatar da Sarkin Maru, Alhaji Abubakar Chika Ibrahim, da hakimin garin Kanoma, Alhaji Ahmad Lawal, ba tare da bata lokaci ba.

A wani jawabi dauke da sa hannun darakta janar na harkokin labaran gidan gwamnati, Alhaji Yusuf Idris, a dakatar da shugabannin biyu ne biyo bayan yawan korafe-korafe game da su akan zargin cewa suna da hannu a lamarin ta’addanci da fashi da makami.

Yace za a ci gaba da dakatar da sarkin da hakimin har sai anji sakamakon binciken farko daga kwamitin bincike.

Don haka, an umurci Sarkin da ya mika motocin masarautar da dukkanin kayayyakin gwamnati ga babban hakiminsa, yayinda aka nemi dakataccen hakimin ya mika mulki ga babban mai gari.

KU KARANTA KUMA: Hawan Sallah: Yan sanda sun kama yan daba 10 a Kano

A baya Legit.ng ta rahoto cewa cewa yan bindiga sun kashe mutum 16 a yankin Kanoma da ke karamar hukumar Maru da ke Zamfara a ranar Sallah.

Da yake tabbatar da lamarin a wani jawabin manema labarai a Gusau a ranar Laraba, 5 ga watan Yuni, Darakta Janar labaran gwamnan jihar, Yusuf Idris yace gwamnan ya ziyarci garin domin yi masu jaje.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel