Hotuna: Kalli yadda aka gudanar da bukin karamar Sallah a garin Bauchi

Hotuna: Kalli yadda aka gudanar da bukin karamar Sallah a garin Bauchi

A jihar Bauchi, kamar kowacce shekara an gudanar da bukin karamar Sallah. A wannan shekarar ma, bukukuwan Sallar sun fara ne jim kadan bayan isowar mai martaba Sarkin Bauchi, Dr. Rilwanu Sulaiman Adamu da kuma gwamnan jihar, Sanata Bala Muhammad (Kauran Bauchi) a fadar Sarkin da ke Bauchi.

Kamar kowacce shekara, tsarin hawan Sallar a jihar Bauchi bai faye sauyawa ba, ana hawan ne a tsarin tawaga bayan tawaga, amma dai, tawagar maharba ke fara baje kolinsu, ta hanyar harbe harben bindiga tun daga isowar Sarki fadar daga masallaci.

KARANTA WANNAN: Buhari zai cika alkawaran da ya daukar ma yan Najeriya – IBB ya bayar da tabbaci

Kusan kowacce tawaga ta mahaya dokuna ko matafiya a kasa, na karkashin wani mai rike da sarautar gargajya a jihar, walau Hakimi, mai Gunduma, mai Littafi ko kuma Dagaci. Gaba daya tawagar na jerawa ne, yayin da ta farko ta shiga ta kai caffa ga sarki, za ta fita domin baiwa tawagar da ke binta baya damar shiga, haka dai har kusan tawaga 50 su kammala kai gaisuwa.

Duba hotunan hawan sallar a kasa:

Hotuna: Gwamna Bala Muhammad tare da Sarkin Bauchi, Rilwanu

Hotuna: Gwamna Bala Muhammad tare da Sarkin Bauchi, Rilwanu
Source: Original

Hotuna: Sabon gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad

Hotuna: Sabon gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad
Source: Original

Hotuna: Tawagar Madakin Basuchi hakimin Kasar Ganjuwa

Hotuna: Tawagar Madakin Basuchi hakimin Kasar Ganjuwa
Source: Original

Hotuna: Masu busa kakaki

Hotuna: Masu busa kakaki
Source: Original

Hotuna: Tawagar Wakilin birnin Bauchi

Hotuna: Tawagar Wakilin birnin Bauchi
Source: Original

Hotuna: Tawagar Baraden Bauchi

Hotuna: Tawagar Baraden Bauchi
Source: Original

Hotuna: Kalli yadda aka gudanar da bukin karamar Sallah a garin Bauchi

Hotuna: Kalli yadda aka gudanar da bukin karamar Sallah a garin Bauchi
Source: Original

Hotuna: Wata tawaga yayin kai caffa ga Sarki da Gwamna

Hotuna: Wata tawaga yayin kai caffa ga Sarki da Gwamna
Source: Original

Hotuna: Sarkin Bauchi, yana dagawa masu hawan sallah hannu

Hotuna: Sarkin Bauchi, yana dagawa masu hawan sallah hannu
Source: Original

Hakika akwai kayartawa da annashuwa, kallon hawan Sallah a jihar Bauchi, za ka ga kowa cikin ado, a saman dokuna ko a kafa. Yayin da su kuma jami'an tsaro ke safa da marwa ko ina domin tabbatar da tsaro ga al'ummar da ke kallon hawan sallar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel