Za’a fara noman kwakwar manja a Zamfara, inji Matawalle

Za’a fara noman kwakwar manja a Zamfara, inji Matawalle

-Jihar Zamfara wacce aka sani kan gaba wurin harkokin noma za ta fara noman kwakwar manja, zance daga bakin gwamanan jihar Bello Matawalle.

-Gwamnan ya shaidawa yan jarida cewa zai mayar da hankali wurin farfado da harkokin noma a jihar ta Zamfar domin abinci ya wadata ba tare da yankewa ba.

Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya sanar cewa nan bada jimawa ba jiharsa zata fara noman kwakwakar manja.

Gwamnan ya bada wannan sanarwa ga manema labarai ranar Alhamis a Gusau babban birnin jihar, inda ya ce gwamnatinsa za ta maida hankali akan harkokin noma kana za ta bada kulawa ta musamman kan noma kwakwar manja.

Za’a fara noman kwakwar manja a Zamfara, inji Matawalle

Za’a fara noman kwakwar manja a Zamfara, inji Matawalle
Source: Getty Images

KU KARANTA:Shin ko me ya hana tsoffin shugabannin Najeriya zuwa wajen rantsar da Buhari?

“ Zamu hada hannu da kasashen waje domin kawo noman kwakwar manja jiharmu. Habbaka harkokin noma a jiharmu na daga cikin kudurorinmu domin samar da wadatar kayayyakin gona.

“ Ya kasance wajibi a garemu na mu sanya makudan kudade domin farfado da harkokin noma a jiharmu, bisa la’akari da daidaicewar lamarin saboda rikicin yan bindiga da ya sa jihar nan a gaba.

“ Gwamnati za ta farfado da aikin Bakalori musamman domin noman rani, a dalilin yin wannan zai samar da wadatar abinci tsawon shekara ba tare da yankewa ba. Kazalika zamu fito da tsarin samar da lantarki saboda manyan kamfanonin mu.” Inji gwamnan.

Gwamnan wanda ya sanya dokar ko ta kwana a fannin ilimi, ya shaidawa Zamfarawa cewa zaiyi iya bakin kokarinsa wajen ganin cewa jiharsu bata kasance cikin jerin jihohin dake fama da matsalar samar da ingantaccen ilimi ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel