Sabon gwamnan Zamfara ya sadaukar da albashinsa ga gidan marayu

Sabon gwamnan Zamfara ya sadaukar da albashinsa ga gidan marayu

Sabo gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ce zai sadaukar da rabin albashinsa ga gidan marayu na garin Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Matawalle ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin wata ziyara ta bazata da ya kai gidan marayun, wacce kuma ita ce ta kasance ziyarasa ta aiki ta farko a wajen gidan gwamnati.

"Daga lokacin da za a fara biya na albashi a matsayin gwamna, na yi umarnin ake tura rabinsa zuwa wannan gidan marayu.

"Na zama uba ga duk yaran dake gidan nan, zan ci gaba da kulawa da walwalar su daga wannan karamar sallar mai zuwa.

Sabon gwamnan Zamfara ya sadaukar da albashinsa ga gidan marayu

Bello Matawalle
Source: Facebook

"Zan yi amfani da kudi na domin dinka musu tufafi da naman da zasu ci, da kuma duk wani abu da zai saka su farin ciki yayin bikin sallah," a cewar sa.

DUBA WANNAN: Mun murkushe kungiyar Boko Haram, ba zata kara dawowa ba - Buratai

A kan shirin da yake yiwa manema labarai a jihar, gwamnan ya ce zai taimaka wa kungiyar 'yan jaridu (NUJ) tare da kulla mu'amala me kyau da su.

"Ba zan tsaya ga iya taimakon NUJ da mambobinta kadai ba, zan tabbatar na samar wa da kungiyar hanyoyin da zata ke samun kudin shigowa domin ta dogara da kan ta," a cewar Matawalle.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel