Gwamnoni 12 da suka sauka daga kan kujerar mulki

Gwamnoni 12 da suka sauka daga kan kujerar mulki

-Gwamnoni 12 ne daga jihohi 29 da akayi zabe a ranar 9 ga watan Maris, 2019 suka sauka daga kan kujerarsu a jiya Laraba domin mika ragamar zuwa ga sabbin gwamnoni.

-Akasarin gwamnoni sunyi nasarar kammala wa'adin mulkin shekara 8 kamar yadda yake acikin kundin tsarin dokokin Najeriya.

Gwamnoni 12 ne suka sauka daga kan mulkin jihohinsu a jiya bayan wasu daga cikinsu sun kammala wa’adin mulki na shekara 8 kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tsara.

Da dama daga cikinsu wadanda suka cika wa’adin mulkin nasu na shekara 8 da ma wadanda suka sha kasa bayan sunyi wa’adi guda daya kacal sun mika karagar mulki zuwa ga sabbin gwamnoni domin cigaba daga inda suka tsaya.

Gwamnoni 12 da suka daga kan kujerar mulki

Gwamnoni 12 da suka daga kan kujerar mulki
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Bikin rantsar da gwamnoni : PDP tayi rawar gani ta doke APC inda ta samu kujeru 15 cikin 29

Gwamnonin da suka yi murabus sun hada da; Rochas Okorocha na Imo, Akinwunmi Ambode na Legas, Ibikunle Amosun na Ogun, Kashim Shettima na Borno da Jibrilla Bindow na Adamawa.

Bugu da kari akwai, Abubakar Bello na Neja, Muhammad Abdullahi Abubakar na Bauchi, Umaru Tanko Al-Makura na Nasarawa, Ibrahim Danwambo na Gombe, Abdulaziz Yari na Zamfara da kuma Ibrahim Gaidam na Yobe.

Sabbin gwamnoni wadannan jihohin su ne:

Ahmadu Fintiri (PDP, Adamawa), Bala Muhammad (PDP, Bauchi), Babagana Zulum (APC, Borno), Inuwa Yahaya (APC, Gombe), Emeka Ihedioha (PDP, Imo), Abdulrahman Abdulrazaq (APC, Kwara), Babajide Sanwo-Olu (APC, Legas), Abdullahi Sule (APC, Nasarawa), Dapo Abiodun (APC, Ogun), Seyi Makinde (PDP, Oyo), Mai-Mala Buni (APC, Yobe) da kuma Bello Matawalle (PDP, Zamfara).

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel