Sakataren Ambode ya yi kaca-kaca da gwamnatinsa

Sakataren Ambode ya yi kaca-kaca da gwamnatinsa

-Sakataren Ambode ya furta kalaman suka da caccaka ga gwamnatin Ambode inda ya kirata da gwamnati mafi muni a tarihin siyasar Legas.

-Mista Tunji Bello yace, ba wai gwamna Ambode bai yi aikin komi bane amma tsare-tsare bayar da ayyukan ne ya sha bambam da na gwamnatocin da suka gabata.

Mista Tunji Bello wanda shine sakataren gwamnatin Ambode wato SSG ya yi kaca-kaca da gwamnatin Akinwunmi Ambode inda ya ce a tarihin siyasar Legas ba’a taba samun gwamnati mafi muni kamarta ba.

Bello ya fadi cewa, gwamnatin Ambode bata da kwarewar sanya ayyuka wuraren da yakamata su kasance da kuma tsari na musamman domin cigaban jama’arsu.

Sakataren Ambode ya yi kaca-kaca da gwamnatinsa

Sakataren Ambode ya yi kaca-kaca da gwamnatinsa
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Bikin rantsar da gwamnoni : PDP tayi rawar gani ta doke APC inda ta samu kujeru 15 cikin 29

A wani batu da ya samu sanya hannun sakataren da kansa, mai taken ‘lokacin ya yi na yin bankwana ga abokan aikina’. Sakataren na cewa: “ Lokacin yin bakwana ga abokan aikina yayi, komi yayi farko to tabbas zai yi karshe. Ya zama wajibi in mika godiyata ga gwamnanmu Akinwunmi Ambode bisa wannan dama da ya bamu tsawon shekaru hudu da suka shude.

“ Ya zama tilas a garemu mu gode masa akan kokarin da yayi wurin jan akalar jihar Legas zuwa matakin da take a yau. Duk wani yabo da godiya a bangaren wannan gwamnatin shi yakamata ayi mawa.

“ Da yake yanzu zamu rabu tare da barin mulki, zai kyautu a ce mu duba wasu daga cikin kurakuranmu domin gyara saboda wurin da dayanmu kan iya tsintar kansa ko dan gaba.

“ Babbar matsalar wannan gwamnatin tamu ita ce, rashin tsara ayyuka yadda yakamata su kasance a tsarin demokradiya. Ayyuka da dama an bada su ne ba tare duba mutanen da suka dace a baiwa ba.

“ Idan mu kayi waiwaye zuwa ga gwamnatin da ta gabata zamu ga cewa duk da ayyukan da wannan gwamnatin ta gwamna Ambode tayi bamu yi kokari ba. A dalilin hakan ne yasa nace wannan mulkin na Ambode shi ne mafi muni a tarihin siyasar jihar Legas. Duk da haka ba zamu fasa godiya da fatan alheri ga mai girma gwamna ba.” A cewar Bello.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel