Zan shahara fiye da Rahama Sadau da Ali Nuhu a Kannywood - Rahama Kumo

Zan shahara fiye da Rahama Sadau da Ali Nuhu a Kannywood - Rahama Kumo

Wata sabuwar jarumar shirya fina-finan Hausa, Rahama Audu Ibrahim Kumo, da aka fi sani da Rahama Kumo a gajarce, ta bayyana cewa, tana ji a jikinta, za ta shahara fiye da jaruma Rahama Sadau da jarumi Ali Nuhu.

A tattaunawar Rahama Kumo da Legit.ng TV Hausa, a yayin da suke daukar wani sabon shirin mai suna 'Rayuwar Hanifa', a jihar Bauchi, ta ce, "Nima zan bi duk matakan da manyan jaruman suka bi, kamar Rahama Sadau, Ali Nuhu, Abdul M Sharif da sauransu har suka shahara, ina da yakinin wata rana zan fi su shahara."

KARANTA WANNAN: Hukuncin Zamfara: Ba mu da zabi sai dai mu amince da hukuncin kotu - APC

Karanta cikakkiyar tattaunawa tsakanin Rahama Ibrahim Kumo da Legit TV Hausa:

Legit TV Hausa: Mai kallo zai so ya san takaitaccen tarihin ki, da kuma yadda aka yi har kika shigo wannan masa'anta ta Kannywood.

Rahama Kumo: Assalamu Alaikum jama'a, ni dai sunana Rahama A Ibrahim Kumo, an haife ni a garin Kumo da ke jihar Gombe, inda na yi karatun firamre har zuwa makarantar gaba da sakandire a cikin jihar.

Legit TV Hausa: Ga shi dai ke Likita ce, ko me ya ja ra'ayinki har kika yanke hukuncin shiga wannan masana'anta ta shirya fina finan Hausa?

Rahama Kumo: Gaskiya na so fina-finan Hausa tun ina 'Nursery School', tun ana kallo a gidanmu da TV mai baki da fari, kamar dai 'Rainbow', kuna kallo yana rawa. Tun muna kallo ana hanamu na ke jin sha'awar shiga wannan sana'a ta fina finan Hausa.

Legit TV Hausa: A lokacin da kika gabatarwa iyayenki da 'yan uwanki wannan bukata ta son shiga wannan masana'anta ta shirya fina finan Hausa, ya suka ji, wacce amsa kika samu daga gare su?

Rahama Kumo: Gaskiya ansha fama, domin ranar da na tunkari mahaifiyata da wannan maganar, ta gargadeni akan kar na kuskura na kara zuwa mata da makamanciyarta ma damar ina son farin cikinta. Wannan ya sa na hakura a lokacin.

Legit TV Hausa: Kina nufin kin shigo masana'antar ba tare da amincewar mahaifiyarki ba?

Rahama Kumo: A'a, ta amince dari bisa dari. Abinda ya faru kuwa shine; bayan wani dan lokaci da sanar da ita burina, sai na je wajen kanwar mahaifina, na sanar da ita muradina, ita ta fahimce ni. Sai ta je ta samu mahaifiyata suka tattauna, a nan ne mahaifiyata ta fahimce ni, har kuma ta sanya mun albarka a cikin wannan hurin nawa.

Legit TV Hausa: Kamar yadda kusan kowanne sabon jarumi ya ke tunani, yakan ce akwai wani jarumi ko jaruma da ya ke so ya zama kamarsa, ko ke ma kina da wani jarumi ko jaruma da kike so ki zama kamarsa ko kamarta?

Rahama Kumo: Kwarai, tun kafin na fara, akwai jaruman da suke burge ni, har na ke son zamowa kamarsu. Na daya akwai Rahama Sadau, akwai Sarki Ali Nuhu, sai kuma Abdul M Sharif. A zahirin gaskiya, nakan ji a raina cewa, wata rana zan shahara fiye da ita Rahama Sadau, ko shi kansa ma sarki Ali Nuhu. Zan bi matakan da suka bi, har suka cimma shahararsu.

Legit TV Hausa: Lokacin da kika shigo wannan masana'anta, da wanne Film kika fara?

Rahama Kumo: Na fara da wani film mai suna 'Mati a Zazzau', daga nan na fito a wani shiri mai suna 'Daren Aure,' sai kuma film din 'Rayuwar Hanifa' wanda shi ne na fi taka rawa sosai, a takaice dai ni ce ma Hanifar. Sannan kuma na fito a wakoki da dama.

Legit TV Hausa: Mukaddara yau kin shahara fiye da wadancan jarumai da kika lissafa, kuma har kika yi aure kika haifi diya mace, ko zaki barta ta shiga wannan harka ta fina-finan Hausa?

Rahama Kumo: Tabbas nima zan barta kamar yadda nima iyayena suka barni. Domin itama bansa wacce iriyar gudunmowa zata kawo a masana'antar ba, zan mata fatan alkairi da kuma bata duk gudunmowar da take bukata.

Daga karshe, sabuwar jarumar, ta yi kira ga masu kallon fina-fina Hausa da ma daukacin 'yan Nigeria da masu kallonsu a kasashen ketare, da su daina daukar 'yan film a matsayin masu aikata abubuwan da suke nuna a film a zahirance.

"Su sani cewa, muna haska rayuwar wasu al'umma ce, domin fadakarwa, nishadantarwa da kuma ilmantarwa, bai kamata su rinka tunanin ko a zahirance halinmu ke nan ba."

Hotunan Rahama A Ibrahim Kumo:

Zan shahara fiye da Rahama Sadau da Ali Nuhu a Kannywood - Rahama Kumo
Zan shahara fiye da Rahama Sadau da Ali Nuhu a Kannywood - Rahama Kumo
Asali: Original

Rahama Kumo
Rahama Kumo
Asali: Original

Zan shahara fiye da Rahama Sadau da Ali Nuhu a Kannywood - Rahama Kumo
Zan shahara fiye da Rahama Sadau da Ali Nuhu a Kannywood - Rahama Kumo
Asali: Original

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu. Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Zan shahara fiye da Rahama Sadau da Ali Nuhu a Kannywood - Rahama Kumo | Legit TV Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel