‘Yan sanda sun kama soja hudu da wasu mutane 84 akan zargin aikata fashi da makami

‘Yan sanda sun kama soja hudu da wasu mutane 84 akan zargin aikata fashi da makami

-Yan sanda a jihar Borno sun damke jami'an soji hudu tare da wasu yan ta'adda 84 akan zargin laifukan da suka shafi fashi da kuma garkuwa da bil adama.

-Kwamishinan yan sandan jihar Borno Ndatsu Muhammad shine ya bamu tabbacin wannan kame da jami'an yan sandan su kayi a ranar Alhamis.

‘Yan sanda a jihar Borno ranar Alhamis sun kama jami’an soji hudu akan zargin aikata fashi da makami. Sojojin wadanda suka bayyana cewa suna karkashin tawagar Operation Lafiya Dole ne dake Borno an kama su tare da wasu mutum 84 wadanda ake zargi da aikata miyagun laifuka.

Da yake shelantawa manema labarai batu, sabon kwamishinan yan sandan jihar, Muhammad Ndatsu yace kama wadannan yan fashi ya zo ne bayan mako biyu da kaddamar da atisayen “Operation Puff Adder” wanda Sufeto yan sanda ya gabatar a jihar.

‘Yan sanda sun kama soja hudu da wasu mutane 84 akan zargin aikata fashi da makami
‘Yan sanda sun kama soja hudu da wasu mutane 84 akan zargin aikata fashi da makami
Asali: Depositphotos

KU KARANTA:EFCC ta maka wani dan kasuwa kotu akan badakkalar N115m

Ndatsu yace, a lokacin da sufeton ya kaddamar da wannan atisayen na Operation Puff Adder a Borno ya shaidawa mutananen jihar cewa masu aikata muggan laifuka ba su da sauran wurin buya a jihar Borno.

Ya kuma ce, nasararorin da ya samu tun shigarsa ofis nada nasaba ne bisa bin tsare-tsare babban sufeton yan sanda da ya ke yi.

Bayan an kaddamar da Operation Puff Adder rundunarmu ta fara aiki gadan gadan, hakan ne ya bamu nasarar damke wasu daga cikin gawurtattun yan ta’adda a sassa daban daban na jihar nan.

A yanzu haka, “yan sandan Borno sun kama mutum 88” wadanda ake kan bincikensu inda ake zarginsu da laifin fashi da makami da kuma sauran miyagun laifuka da suka hada da garkuwa da mutane, fataucin miyagun kwayoyi da kisan kai.

Bugu da kari, “a ranar 13 ga watan Mayu, 2019 jami’an da ke yaki da fashi da makami na hukumar yan sanda wato SARS suka kama wani soja Kofur Hilary Ozuoma Godwin mai lamba 09NA/63/3117 wanda ke aiki da bataliyar Monguno da laifin fashi ga wani Ibrahim Muhammad tare da abokin aikinsa.” Inji kwamishinan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel