Madalla: An kama ‘yan baranda 20 a jihar Sokoto

Madalla: An kama ‘yan baranda 20 a jihar Sokoto

-Jami'an yan sanda a jihar Sokoto sun yi nasarar cafke yan baranda 20 a ranar Talata.

-A cewar kwamishinan yan sandan jihar, wannan nasarar ta samu ne sanadiyar taimakon sauran hukumomin tsaro dake jihar wadanda ke taimakawa jami'an yan sanda domin kawo karshe yan baranda a jihar ta Sokoto.

Mutane 20 wadanda ake zargin cewa ‘yan baranda ne sun shiga hannun jami’an ‘yan sanda ranar Talata a jihar Sokoto.

Mutanen da aka samu nasarar cafkewa bayan wani rangadi da hukumar yan sanda tayi a fadin jihar an kai su babbar shelkwatar yan sandan dake jihar.

Madalla: An kama ‘yan baranda 20 a jihar Sokoto

Madalla: An kama ‘yan baranda 20 a jihar Sokoto
Source: UGC

KU KARANTA:Ku zauna a gida ko ku dandana kudar ku, hukamar ‘yan sanda ta gargadi kungiyar IPOB

Kwamishinan yan sandan jihar, Ibrahim Kaoje yace wannan nasarar ta samu ne sanadiyar jajircewa da kuma hadin kai daga wurin sauran jami’an tsaro dake jihar.

Yace, wadanda ake tuhumar an kama su ne cikin makon da ya gabata tare da bindigogi, kwaya, gatari, tabar wiwi, kakin sojoji da kuma layu.

Kazalika, ya sake nuna mana cewa hadin gwiwar hukumomin tsaro a jihar ya fara haifar da sakamako mai kyau musamman wurin kawo karshe yan baranda a jihar.

Kaoje ya yi kira ga al’ummar jihar Sokoto da su cigaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum kamar yadda suka saba, tareda da basu tabbaci cewa rayukansu da dukiyoyi za su samu tsaron da ya dace.

Ya sake jaddada cewa, tabbas ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro zasu cigaba da zakulo ‘yan baranda da sauran masu tada kayar baya a fadin jihar wadanda ke hana al’umma zama lafiya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel