Kannywood: Kotu ta janye dokar kama wata shahararriyar yar fim din Hausa da ta bayar a baya

Kannywood: Kotu ta janye dokar kama wata shahararriyar yar fim din Hausa da ta bayar a baya

-Kotu ta janye dokar da ta sanya kan cewa lallai jami'an yan sanda su kawo mata Hadiza Gabon.

-Gabon ta karyata cewa ta roki jarumi Nabaraska

Kotun majistare wacce ke garin Kano ta janye dokar da ta bayar ga kwamishinan ‘yan sanda na ya kamo Hadiza Aliyu Gabon.

Idan bamu manta ba Mustapha Badamasi wanda aka fi sani da Nabraska shine yayi karar jarumar akan zargin taci zarafinsa.

Kannywood: Kotu ta janye dokar kama wata shahararriyar yar fim din Hausa da ta bayar a baya

Kannywood: Kotu ta janye dokar kama wata shahararriyar yar fim din Hausa da ta bayar a baya
Source: Facebook

KU KARANTA:Azumin Ramadana: Gwamnatin jihar Sakkwato ta bude cibiyoyi 138 domin bude baki

Bayan Nabraska ya shigar da karar jarumar zuwa kotun majistare dake Kano, sai kotun ta aikawa Hadiza da sammaci yayin da taki bayyana a gaban kotun.

Shugaban wannan kotun, Muntari Dandago shine ya baiwa kwamishina Muhammad Wakili umarnin a kamo masa wannan jaruma saboda taki amsa gayyatar kotu.

A wani labari mai kama da wannan, Hadiza Aliyu Gabon ta karyata labarin da ake yadawa a kanta na cewa wai 'yan sanda sun kamata sannan kuma ta durkasa har kasa domin neman afuwar Nabraska.

Jarumar tayi watsi da wannan labari inda take cewa, " Babu dan sandan da ya kama ni, kuma ni da Mustapha mun yi sulhu ne a harabar kotu amma ban durkusa ma kowa ba. Masu yada wannan labari suna kokarin bata min suna ne kawai."

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel