Rashin tsaro: Shehu Sani yayi magana mai zafi akan harin da ya kashe mutum 30 a Katsina

Rashin tsaro: Shehu Sani yayi magana mai zafi akan harin da ya kashe mutum 30 a Katsina

-Shehu Sani ya yi kira ga gwamnati ta tashi tsaye domin magance matsalar tsaro musamman a yankin arewacin Najeriya.

-Sanata Abdullahi Ibrahim Gobir mai wakiltar Sakkwato ta Gabas yayi korafi game da halin da yankinsa ke ciki na fuskantar rashin tsaro.

Dan majalisar dattawa mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani yayi magana akan harin da aka kai kananan hukumomi uku dake jihar Katsina.

Rahatonni na nuna cewa mutum 18 ne suka mutu a kauyen Yargamji dake karamar hukumar Batsari, mutum 5 a karamar hukumar Danmusa da kuma mutane 11 a kauyen Sabon Layi dake karamar hukumar Faskari.

Rashin tsaro: Shehu Sani yayi magana mai zafi akan harin da ya kashe mutum 30 a Katsina
Rashin tsaro: Shehu Sani yayi magana mai zafi akan harin da ya kashe mutum 30 a Katsina
Asali: Twitter

KU KARANTA:Azumin Ramadana: Gwamnatin jihar Sakkwato ta bude cibiyoyi 138 domin bude baki

Dan majilisan ya sake yin magana akan sace fasto da akayi a garin Kaduna tare da wasu mabiyansa mutum 15 a ranar Lahadin da ta gabata.

Ga abinda ya fadi ta hanyar shafinsa na twitter, “ Ranar Lahadi a garin Kaduna ‘yan baranda sun kai farmaki cocin ECWA dake Dankande inda suka sace fasto tare da mutum 15 daga cikin masu bauta a cocin.

“ Yanzu kuma gashi ‘yan bindiga sun kai hari Batsari da wasu kananan hukumomi biyu a jihar Katsina. Wannan shine hakikanin abinda ke faruwa damu.”

A baya Shehu Sani yayi kira kan cewa ba addu’a ce kadai zatayi mana maganin wannan matsalar rashin tsaro dake addabarmu ba.

A fadarsa, “ Idan mukayi aiki tare da addu’a to hakan zai sa matsalarmu ta kau, amma idan mukayi addu’a kawai ba tare da yin abinda ya dace ba za mu ga sauyi ba.”

A wani labarin mai kama da wannan kuwa, dan majalisa mai wakiltar Sakkwato ta Gabas, sanata Abdullahi Ibrahim Gobir a ranar Talata ya roki majalisar da ta kawo karshe kashe-kashe da garkuwa da mutanen dake addabar gabashin Sakkwato.

A cewarsa, “ Garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a yankin Sakkwato ta gabas inda a halin yanzu mutane 13 ke hannun masu garkuwa da mutane kuma suna bukatar kudade masu yawa a matsayin fansa.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel