Ta leko ta koma: Hukumar INEC ta karbe takardar shaidar lashe zabe daga hannun yan majalisa biyu a Kaduna

Ta leko ta koma: Hukumar INEC ta karbe takardar shaidar lashe zabe daga hannun yan majalisa biyu a Kaduna

-Kotu ta soke nasarar Haruna Aliyu da kuma Ibrahim Ismail a zaben yan majalisar dokokin jihar Kaduna da ya gabata.

-Hakan ya biyo bayan saba doka da jam'iyar APC tayi yayin kai sunayen wadanda suka lashe zaben fidda gwani a karkashin jam'iyar tasu.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC a ranar Talata ta karbe shahadar da ta baiwa biyu daga cikin sabbin yan majalisar dokokin jihar Kaduna. Wadannan yan majilasar dai sune, Haruna Aliyu wanda aka fi sani da Chakis sai kuma Ibrahim Ismail.

Haruna Aliyu yana wakiltar Kaduna ta Arewa 2 (Kawo) yayin da shi kuma Ismail Ibrahim yana wakiltar Kaduna ta Kudu 2 (Tudun Wada).

Ta leko ta koma: Hukumar INEC ta karbe takardar shaidar lashe zabe daga hannun yan majalisa biyu a Kaduna

Ta leko ta koma: Hukumar INEC ta karbe takardar shaidar lashe zabe daga hannun yan majalisa biyu a Kaduna
Source: Getty Images

KU KARANTA:Yanzun nan: Yan bindiga sun kai mumunan hari Dan Musa, Faskari da Batsarin jihar Katsina

Wadannan mutane biyu sun fafata a zaben fitar da gwani karkashin jam’iyar APC a watan Oktoban 2018. Inda abokan karawarsu su kayi nasara akan su, Yusuf Salihu mai kuri’a 104 shine ya doke Haruna Aliyu a zaben yayin da shi kuma Ibrahim Ismail ya sha kashi a hannun Nasiru Usman wanda ya samu kuri’a 49.

Jam’iyar APC bata kai sunayen wadanda suka lashe zaben fidda gwanin ba sai ta kai sunayen Haruna Aliyu wanda ya samu kuri’a 24 da kuma Ibrahim Ismail mai 35 a matsayin yan takarar kujerar majalisar jiha a gundumominsu.

Babbar kotun kasa dake jihar Kaduna karkashin jagoranci, Alkali Z. B Abubakar ta yanke hukuncin cewa Nasiru Usman da kuma Yusuf Salihu kasancewar sune mutane biyu da sukayi nasara a zaben fidda gwani na jam’iyar APC, su ya fi dacewa da su tsaya takara.

A don haka kotun ta musanya Haruna Aliyu da Yusuf Salihu yayin da shi kuma Nasiru Usman ya canji Ibrahim Ismail a matsayin yan majalisu masu wakiltar Kaduna ta Arewa (Kawo) da kuma Kaduna ta Kudu (Tudun Wada). Kuma tuni INEC ta karbe takardar shaidar ta baiwa wadanda kotu tayi umarni a bawa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel