Hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta yi gargadi ga CP Wakili

Hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta yi gargadi ga CP Wakili

-Hukumar NDLEA ta nuna rashin jin dadin ta akan abinda kwamishinan yan sandan jihar Kano keyi na shiga huruminta.

-Kwamanda hukumar a jihar Kano ya nemi kwamishinan da ya tsaya matsayinsa ko kuma kotu ta shiga tsakaninsu.

Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa wato NDLEA ta gargadi kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Muhammadu Wakili kan ya fita daga sha’anin yaki da fataucin miyagun kwayoyi ko kuma ya fuskanci hukuncin shari’a.

Kwamandan hukumar a jihar Kano, Ibrahim Abdul yace, “ sashe na 3 (1) na kundin dokokin hukumar NDLEA ya basu damar kasancewa jagoran dukkanin al’amura da suka shafi tu’ammali da muggan kwayoyi a Najeriya.”

Hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta yi gargadi ga CP Wakili

Hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta yi gargadi ga CP Wakili
Source: UGC

KU KARANTA:Ganduje zai sauke mukarrabansa ranar Laraba

Wannan rashin jituwar dai ya zo ne sakamakon furucin da kwamishinan yayi na cewa jami’an ‘yan sanda sun yi nasarar damke kwalayen tramadol 303 cikin makon da ya gabata a jihar Kano.

Da yake zantawa da manema labarai ranar Talata, Abdul yace ‘yan sanda sun karbe wani magani mai suna “diclofenac” wanda ke maganin ciwo jiki amma ba tramadol ba.

Kazalika, Abdul ya kara fayyace mana cewa irin hakan ya taba faruwa a watan Fabrairu inda hukumar yan sanda tayi ikirarin cewa ta karbe kwayar tramadol, ko da muka bincika sai muka samu ashe maganin zazzabin cizon sauro ne da wani makamancinsa.

“ Irin hakan ya taba faruwa a watan Fabrairu inda yace sun kama mota biyu na tramadol. Ko da muka same shi sai yace mana ya tura da su zuwa NAFDAC. Da isar mu NAFDAC sai muka tarar da abu daban da wanda ya fada mana.

“ Babu saniyar ware a shari’a ko ni idan na karya doka dole shari’a zatayi hukuncin mafi dacewa a kaina. Saboda haka ina kira ga hukumar yan sanda da sauran hukumomi da kowa ya tsaya matsayinsa banda wuce gona da iri yayin gudunar da ayyukansu.” Inji kwamandan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Online view pixel