Jami’an sojin ruwan Najeriya sunyi wani gagarumin kame

Jami’an sojin ruwan Najeriya sunyi wani gagarumin kame

-Wasu mutane uku da ake zarginsu da laifin fasa kwauri sun shiga hannun jami'an sojin ruwan Najeriya.

-An kama wadannan mutanen da buhun shinkafa guda 455 akan hanyar Calabar.

Zaratan jami’an sojin ruwan Najeriya sun damke mutum uku wadanda ake zargi da laifin fasa kwaurin buhun shinkafa guda 455 wanda kudinsu ya kai naira miliyan 8 a kan hanyar Calabar.

Kwamandan wannan tawaga da ta cafke mutanen, Komodo Vincent Okeke ya mika su zuwa ga hukumar kwastam a ranar Talata inda yace mutanen sun fito ne daga kasar Kamaru.

Jami’an sojin ruwan Najeriya sunyi wani gagarumin kame

Jami’an sojin ruwan Najeriya sunyi wani gagarumin kame
Source: Facebook

KU KARANTA:Aikin hajjin 2019: Hukumar kula da aikin hajji ta kasa ta fadi jiragen da zasuyi jigilar maniyyatan wannan shekara

“ Farashin shinkafar da muka kama a kasuwa ya kai naira miliyan 8. Amma dai bashi bane abin dubawa a nan, durkeshewar tattalin arzikin da fasa kwaurin ke haifarwa kasar mu shi ne abin dubawa. Yana kara baza yaduwar rashin aikinyi, durkushewar tattalin arzikin kasa, hana gwamnatin samun kudin shiga wanda ya kamata ace tana samu.

“ Hafsin sojin ruwa Najeriya ya bamu umarnin yaki da fasa kwauri har sai mun ga bayansa. Wannan shi ne abinda mukeyi a halin yanzu. Sakon d azan isar zuwa ga masu fasa kwauri shine mu zuba mu da su zamu ga wanda zai fasa. A duk lokacin da muka kama masu laifi irin wannan muna mika sune zuwa ga hukumar kwastam.

“ Tun dawowa ta bamu sake samun wata matsala ba, komi da muke bukata domin gudanar da ayyukan mu an riga da an bamu shi. Mun samu labarin mutumin dake da mallakar wannan kayan da muka cafke. Wani Mista Emmanuel ne dake Uyo, ko shakka babu hukumar kwastam zata nemo shi.” Inji Okeke.

Mataimakin kontrolan kwastam na yankin kudanci, Johnson Gabriel ya yabawa jami’an sojin ruwa da wannan namijin kokarin da sukayi, sannan kuma yace a nasu bangaren kokarin da sukeyi na ganin bayan fasa kwauri na nan har ila yau.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel