Yanzun nan: Yan bindiga sun kai mumunan hari Dan Musa, Faskari da Batsarin jihar Katsina

Yanzun nan: Yan bindiga sun kai mumunan hari Dan Musa, Faskari da Batsarin jihar Katsina

-Yan bindiga su kai hari kananan hukumomi uku a jihar Katsina inda suka kashe mutane dama.

-Kananan hukumomin da wannan harin ya shafa sun hada da, Danmusa, Faskari da kuma Batsari.

Mutane da dama sun mutu sakamakon wani mummunan harin da yan bindiga suka kai a kananan hukumomin Dan Musa, Faskari da Batsarin jihar Katsina.

Wata majiyar da ta shaidawa wakilinmu yadda lamarin ya faru tace, ‘yan bindigan sun kawo wannan harin ne a saman babura inda suka kashe dimbin mutanen da ba su san hawa ba balle sauka.

Yanzun nan: Mutane da dama sun mutu a sakamakon harin yan bindiga a kananan hukumomi uku dake Katsina
Yanzun nan: Mutane da dama sun mutu a sakamakon harin yan bindiga a kananan hukumomi uku dake Katsina
Asali: Twitter

KU KARANTA:Aikin hajjin 2019: Hukumar kula da aikin hajji ta kasa ta fadi jiragen da zasuyi jigilar maniyyatan wannan shekara

A garin Sabon Layi dake karamar hukumar Faskari, yan bindigan sun shige shi ne da asubah da bindigogi inda suka kashe mutane 11.

Kazalika, kakakin hukumar yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah yace “labarin da yazo gaban hukumar yan sanda shine mutum guda daya kawai aka harba wanda kuma a halin yanzu yana asibiti ana bashi kulawa. Sai dai kuma anyi awon gaba da dabbobi masu tarin yawa yayinda aka bar mutum guda a kwance shame-shame.”

A kauyen Mara Zamfarawa dake Dan Musa mutane 5 aka kashe a safiyar Talata tare da yin gaba da dabbobi masu yawa. Mazauna wannan kauye sun ce ‘yan bindiga sun farma manoma wadanda ke a gonarsu suna aiki.

A kauyen Yar Gamji kuwa wanda ke karamar hukumar Batsari, mutane 10 yan bindigan suka kashe. Wannan harin ya auku ne a ranar Talata. A daidai lokacin hada wannan rahoton hukumar yan sanda bata da cikakken bayani akan sauran shiyoyi biyun da wannan harin ya shafa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel