Menene makomar Gareth Bale a Real Madrid?

Menene makomar Gareth Bale a Real Madrid?

-Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid na neman yadda zatayi da Gareth Bale kafin kakar wasa mai zuwa.

-Dan wasan da ya fito daga kasar Wales na da sauran kwantiragi da kungiyar Real Madrid har zuwa 2022.

Kakar bana ta karewa Gareth Bale ba tare da dadi ba yayin da ya zauna a benci wasan karshe na gasar La Ligar bana.

Bayan sun kare a mataki na uku da maki 19 tsakaninsu da zakarun gasar La Ligar ta bana wato Barcelona. Kocin kungiyar Zinedine Zidane na kokarin gina sabuwar tawaga domin fuskantar kalubalen dake tafe.

Mece ce makomar Gareth Bale a Real Madrid?

Gareth Bale
Source: Getty Images

KU KARANTA:Wata sabuwa: Gawar jaririya tayi sama ko kasa a wani asibiti dake Ondo

Bale ya nuna rashin jin dadin sa a wasa na karshe yayin da aka ajiye shi a benci. Ya lashe shekara shida a kasar Spain, inda ya lashe kofuna 13 wanda ya bashi damar yin kamo dan wasa Phil Neal a mastayin dan Birtaniya da ya fi kowa lashe kofuna.

Dan wasan ya cika alkawarin da ya dauka lokacin da ya je Madrid cewa “ zai zama dan wasan Birtaniya da ya fi kowa taka rawa a kasashen ketare.”

Zabin Zidane na ya raba gari da dan wasan yana cike da rudani ganin irin girman yarjejeniyarsa. Bale yana da fam miliyan 55 a cikin kwantarginsa wanda zai kare a 2022. Idan aka bi dalla-dalla, baki daya albashin da kungiyar Huddersfield Town ta firimiyar Ingila ta biya yan wasanta a kakar 2017-2018 fam miliyan 62.6 ne.

Saboda indai Bale yana son barin kulob din to sai fa Real Madrid ta tallafawa kulob din da yake son sayan sa wajen rage darajarsa.

Ko dai ya kasance an rage kudin sayensa, ko a rage masa albashi ko kuma a bayar da aronsa. Babu abinda ke da sauki cikin wadannan, a daidai lokacin da Zidane ke son yiwa kungiyar garambawul, wanda zai hada da zuwan Hazard daga Chelsea.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel