Limamin cocin da ya ce zan mutu ya roke ni gafara - Sheikh Sharubutu

Limamin cocin da ya ce zan mutu ya roke ni gafara - Sheikh Sharubutu

- Babban limamin kasar Ghana, Sheikh Sharubutu yace limamin cocin da yayi masa bushara da mutuwa ya nemi yafiyarsa

- Wani limamin coci mai suna Owusu Bempah ya ce a shekarar 2019 Sheik Sharubutu zai amsa kiran Allah

- Babban limamin ya shaida cewa asalinsa duka daga Najeriya ne

Sheikh Nuhu Sharubutu, wanda ya kasance babban limamin kasar Ghana mai shekara 100, ya bayyana cewa limamin cocin da yayi masa bushara da mutuwa ya nemi yafiyarsa.

Shehin malamin ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da yi sashen BBC Hausa.

A kwanakin baya ne dai aka rahoto cewa wani limamin coci mai suna Owusu Bempah ya ce a shekarar 2019 Sheik Sharubutu zai amsa kiran Allah inda hakan ya jawo ce-ce-ku-ce.

Limamin cocin da ya ce zan mutu ya roke ni gafara - Sheikh Sharubutu
Limamin cocin da ya ce zan mutu ya roke ni gafara - Sheikh Sharubutu
Asali: UGC

Da aka tambayayi Malamin ko ya ya ji game da maganar wani faston kan cewa a shekarar 2019 zai mutu? Sai ya ce "Ai abu ne na Allah. Shugaban kasa ma da kansa ya yi masa fada. 'Yan uwansa ma sun yi masa fada.''

Sheikh Sharubutu ya bayyana cewa Faston ya zo har gidansa inda ya nemi gafara a kan furucin sa.

KU KARANTA KUMA: Hukumar DSS ta gargadi masu kokarin juyin mulki gabannin rantsar da Buhari

Babban limamin ya shaida cewa asalinsa duka daga Najeriya ne. Mahaifinsa daga Kukawa ta jihar Borno, yayinda Mahaifiyarsa kuma ta fito daga Rafindadi a cikin garin Katsina.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel