Daya daga cikin ‘yan matan Chibok ta kammala digiri a kasar Amurka

Daya daga cikin ‘yan matan Chibok ta kammala digiri a kasar Amurka

-Daya daga cikin 'yan matan Chibok mai suna Palmatah Mutah ta kammala karatun digiri a kwalejin kasar Amurka

-Palmatah mai shekara 22 ta kasance daliba ta farko da ta samu wannan matsayi na kammala digiri cikin 'yan matan Chibok

Daya daga cikin ‘yan matan sakandiren Chibok da ‘yan kungiyar Boko Haram suka sace a shekarar 2014 ta samu nasarar kammala karatun digiri a kasar Amurka.

Dalibar mai suna Palmatah Mutah, mai shekara 23 ta tsere ne daga hannun ‘yan Boko Haram ta hanyar dira daga kan babbar motar da ke tafiya yayin da aka kwashi ‘yan matan daga makarantarsu.

Daya daga cikin ‘yan matan Chibok ta kammala digiri a kasar Amurka

Daya daga cikin ‘yan matan Chibok ta kammala digiri a kasar Amurka
Source: UGC

KU KARANTA:Sha’anin tsaro: Sojin Najeriya sun tattauna da takwararsu ta kasar Nijar

Kammala karatun da tayi a kwalejin Northern Virginia Community yazo a daidai lokacin da garkuwa da ‘yan matan Chibok ke cika shekara biyar da wata daya da kwana uku.

Palmatah dai tayi digirinta ne a bangaren kimiyya kuma ita ce daliba ta farko daga cikin ‘yan matan Chibok da akayi garkuwa da su wacce ta samu nasarar kammala digiri kuma dadin dadawa a kasar waje.

A lokacin da akayi garkuwa da daliban, akasarin ‘yan Najeriya sun yi ta mamaki ganin cewa kusan 57 daga cikin ‘yan matan ba su jin turanci, sai kuma ga shi yanzu akasarinsu na zangon karshe na kammala karatun jami’a.

Palmatah ce kadai a cikin su goma ta samu damar samun gurbin karatu a wannan shahararriyar kwaleji bayan da lauyan kare hakkin bil adama wato Emmanuel Ogebe ya dauki nauyin daliban zuwa kasar waje.

A watan Janairun 2016 ne, Palmatah tare da wasu da harin Boko Haram ya rutsa da su wadanda ba ‘yan matan Chibok ba suka fara karatunsu a wannan kwaleji. Daya daga cikinsu ta kammala karatunta tun shekarar bara a bangaren kimiyya wanda shi Palmatah ta karanta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel