Lalong ya kwaikwayi Ganduje, ya kasafta masarautar Jos

Lalong ya kwaikwayi Ganduje, ya kasafta masarautar Jos

-Lalong ya rage karfin sarautar Gbong gbom Jos duk da cewa sarkin bai aminta da batun da jama'a keta yadawa akan lamarin ba

-Gwamnan yayi hakan ne ta hanyar tsige sarakuna Jos ta arewa da Riyom daga karkashin masarautar ta Jos da suke a da

Gwamnatin jihar Filato ta cire masarautun Jos ta arewa da kuma Riyom daga karkashin gamayyar masarautar Jos wacce Sarkin Jos Buba Jacob ke jagoranta.

Mutanen da dama na duban lamarin a matsayin wani yinkuri na takaita karfin ikon sarkin.

A watan Agustan da ya gabata ne gwamna Simon Lalong ya kirkiri wasu hakimai sabbin yayinda kuma ya daga darajar masarautun Jos ta arewa da Riyom.

Lalong ya kwaikwayi Ganduje ya kasafta masarautar Jos
Lalong ya kwaikwayi Ganduje ya kasafta masarautar Jos
Source: UGC

KU KARANTA:Wasu gwamnoni na shiga sharo ba shanu a jihohinsu, inji Dogara

Bayan daga darajar masarautun zuwa daraja ta farko, gwamnan ya mikawa ko wannen su sandar girma.

A wata wasika wacce kwamishinan kananan hukumomi ya rubutawa shugabannin kananan hukumomin Jos ta arewa da Riyom, yace dukkanin sarakunan da aka daga darajarsu zasu iya kaddamar da majalisarsu ta fada domin cigaba da ayyukansu.

Wasikar ta bayyana cewa wannan abu da Lalong ya aikata bai sabawa doka ba. Yana nan kunshe cikin kundin dokokin kananan hukumomi na shekarar 2016 a sashe na 9(1) da kuma sashe na 9(3), inda dokar ke cewa sarki na farko a ko wace karamar hukuma shi zai kasance shugaban sarakunan gargajiya a yankin nasa.

Wannan abu ya haifar da cece-kuce a tsakanin jama’a inda wasu ke ganin gwamnan yayi hakan ne kawai domin ya batar da sunan sarkin Jos.

Sai dai sarki Jacob Buba yayi watsi da wannan magana inda yake cewa ta yawun hadiminsa “ Har yanzu ina nan a matsayina na sarkin Jos. Ko kadan abinda mutane ke yadawa ba gaskiya bane, basu fahimci abinda akayi bane kawai.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel