Wasu gwamnoni na shiga sharo ba shanu a jihohinsu, inji Dogara

Wasu gwamnoni na shiga sharo ba shanu a jihohinsu, inji Dogara

-Dogara ya nuna rashin jin dadinsa gameda yadda gwamnoni keyi a jihohinsu

-A cewar kakakin majalisar, majalisun jihohi nada yanci cin gashin kansu kamar yadda dokar kasa ta tanada

Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara ya caccaki wasu daga cikin gwamnoni saboda sanya baki da suke cikin lamuran majalisa da kuma shari’a a jihohinsu.

Dogara wanda ya fadi wannan maganar wurin wani taro na musamman akan muhimmancin samarwa majalisar jiha gashin kanta ranar Alhamis a Abuja, yace wasu gwamnonin samu ba suyi abinda ya dace jiharsu.

Wasu gwamnoni na shiga sharo ba shanu a jihohinsu, inji Dogara

Wasu gwamnoni na shiga sharo ba shanu a jihohinsu, inji Dogara
Source: Twitter

KU KARANTA: Nadin Emefiele: Wani dan majalisar APC ya mayar wa da Gudaji Kazaure martani

Kakakin yace kasancewar a baiwa majalisa damar cin gashin kanta abu wanda yake a rubuce cikin kundin tsarin mulki kasar nan na 1999, wanda yake kunshe a sashe an 4, 5 da kuma 6.

Yace manufar wadanda suka rubuta wadannan dokoki shine domin a samarwa ko wacce daga cikin rassan gwamnati damar gudunar da wasu abubuwa a karkashin kulawarta ba tare da anyi mata shige ba.

Dogaran ya sake cewa, “ Kasancewar daya daga cikin rassan gwamnati shike kula da harkokin kudin dayan matsala ce babba wacce ta sabawa dokar kasa. Kamata yayi ace ko wane reshe yana gudanar da ayyukansa ne daban kamar yadda doka ta tanadar.

Rashin barin majalisun jihohi suci gashin kansa ya zame mana matsala a jihohinmu, saboda gwamnoni kawai keyi abinda suka ga dama.

Akasarin kudin da gwamnatin tarayya ke turowa jihohi na kasancewa ne a karkashin kulawar gwamnoni a don haka sai yadda sukayi dashi.” Inji Dogara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel