‘Yan siyasa na da hannu cikin tabarbarewar tsaro a Arewa, inji Buratai

‘Yan siyasa na da hannu cikin tabarbarewar tsaro a Arewa, inji Buratai

-Buratai ya zargi yan siyasa da sa hannu cikin tarbarbarewar tsaron arewacin Najeriya

-Babban hafsun sojin Najeriya yace suna da kwararan hujjoji masu nuna cewa yan siyasar da ba suyi nasara a zaben da ya gabata bane ke hura wannan wutar

Babban hafsun sojin Najeriya Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai ya danganta ta’addancin dake addabar arewacin Najeriya da siyasa.

Buratai yace suna da hujjoji kwarara akan cewa yan siyasa na taimakon ta’addanci wanda ya hada da yan bindiga, garkuwa da mutane da kuma wasu matsalolin tsaro dake damun yankin.

Akwai sa hannun ‘yan siyasa cikin tabarbarewar tsaro a Arewa, inji Buratai

Laftanal Janar Tukur Buratai
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Sabbin masarautun Kano: Munyi mubaya’a ga masarautar Gaya, inji wata kungiya dake Wudil

Babban hafsun sojin yayi wannan fashin bakin ne yayin da ya karbi bakuncin shugaban kwamitin soji na majalisar dokoki ta kasa.

“ Tabbas akwai kungiyar Boko Haram har yanzu, duk da cewa mun karyasu gwargadon karfinmu. A wuraren dake a bayyane irin cikin birane, su kan labe ne idan sun kai hari duk don dai a san har yanzu suna nan.

“ A halin yanzu arewacin kasar nan na fuskantar barazanar rashin tsaro. Ko shakka babu wasu yan siyasa ne ke goyon bayan wannan ta’addanci saboda rashin nasarar da sukayi a zabe. A irin nasu tunanin hakan shine ramuwa a garesu, don haka suke haddasa rikicin Fulani da makiyaya, yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

“ In takaita maku zance, akwai sa hannun yan siyasa a cikin wannan matsalar rashin tsaro da muka tsinci kanmu ciki.” Inji Buratai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel