Agogo sarkin aiki: Gwamnan Legas mai barin gado Ambode

Agogo sarkin aiki: Gwamnan Legas mai barin gado Ambode

- Ambode ya bar abinda jama'ar Legas zasu dade suna tunawa dashi ko bayan saukarsa a mulki

- Kwanaki na kara matsowa domin rantsar da sabbin gwamnonin jihohi, ga wasu daga cikin muhimman ayyukan da Ambode yayiwa jihar Legas

A cikin kwanaki kalilan wa’adin mulkin gwamna Akinwumi Ambode zai kare a matsayinsa na gwamnan jihar Legas. Sai dai ko shakka babu gawamnan zai tafi ne jama’ar Legas na kewarsa tare da yaba masa na ayyukan cigaba da ya gudanar cikin shekaru hudu a jihar.

A ranar 29 ga watan Mayun 2015 ne aka rantsar da Ambode a matsayin gwamnan jihar Legas wanda ya karbi akalar mulkin jihar daga hannun Babatunde Raji Fashola wanda shine ministan ayyuka, lantarki da kuma gidaje a yanzu.

Agogo sarkin aiki: Gwamnan Legas mai barin gado Ambode
Agogo sarkin aiki: Gwamnan Legas mai barin gado Ambode
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Talauci: Da kyar Osinbajo ya samu na yarda da Trader Moni - Shugaba Buhari

Mutane da dama na ganin cewa Ambode ba zai iya yin abinda Fashola yayi ba a lokacin mulkinsa. Hakan bai sanya Ambode ya daga hankalinsa ba inda ya cigaba da bin tsare-tsarensa cikin tsanaki wanda hakan ne ma ya bashi damar yin ayyukan da jama’a keta yabawa a halin yanzu.

Ga wasu daga cikin muhimman ayyukan Gwamna Ambode:

Mangance matsalar ranshin tsaro

Domin samar da tsaro a jihar Legas, gwamna Ambode ya kayata sashen bayar da kulawar gaggawa wato RRS na hukumar yan sandan Najeriya inda ya basu N4.675bn tare kuma da gudumawar kayan aiki. Wannan abu ya faru ne a watan Satumban 2015. Daga cikin abubuwan da ya baiwa hukumar yan sanda sun hada da; kananan motoci guda 100, a kori kura kirar guda 55, Toyata land cruiser guda 10, babur kirar BMW 15, jirgin helikopta guda 3 da dai sauransu.

Habbaka sha’ani sufuri

A cigaba da inganta rayuwar jama’ar Legas ta fannin sufuri, gwamnan ya gina katafaren tashar bas ta zamani a Ikorodu. Inda ya sanya masu motoci kirar bas masu dauke da na’aurar sanyaya muhalli wato AC har guda 434. Kari akan wannan gwamnan ya kaddamar da aikin layin dogo wanda zai kasance yana kaiwa da kawowa a birnin Legas kuma zai iya daukar mutum 500,000 a rana.

Inganta kula da laifiyar jama’ar Legas

A wannan bangaren kuwa gwamnan ya samar da motocin daukar masara lafiya wanda kan iya bayar da taimakon gaggawa ga mara lafiya guda 20 da kuma motar kai marasa lafiya asibiti guda 26 wadanda aka raba zuwa manya asiitocin jihar.

Samar da abinci

A fannin abinci kuwa gwamnan ya kulla wata alaka ta noma shinkafa da jihar Kebbi wanda yayi sanadiyar samun shinkafa mai suna Lake. Hakan kuma yan sanya farashin shikafa a kasuwanni Legas ya ragu kuma jama’a suka samu sauki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel