Mutum 1 ya mutu, 3 sun samu rauni sakamakon harin yan bindiga a kauyen Katsina

Mutum 1 ya mutu, 3 sun samu rauni sakamakon harin yan bindiga a kauyen Katsina

-Yan bindiga sun kai mummunan hari a kauyen Wagini dake Batsari a jihar Katsina

-Harin yayi sanadiyar rasuwar mutum daya da kuma raunana mutum uku wadanda yanzu haka suke karbar kulawar asibiti

Yan bindiga a daren Juma’a sun kai hari kauyen Wagini na karamar hukumar Batsari dake jihar Katsina inda suka kashe mutum guda tareda raunana wasu ukun.

Yan bindigan sun kai harin ne tsakar dare inda suka shiga harbe-harbe da kuma sanya wuta akan motocin mazauna karkarar tareda da kona masu gidaje.

Mutum 1 ya mutu, 3 sun samu rauni sakamakon harin yan bindiga a kauyen Katsina
Mutum 1 ya mutu, 3 sun samu rauni sakamakon harin yan bindiga a kauyen Katsina
Asali: Twitter

KU KARANTA:Zamu yi aiki tareda yan sintiri da mafarauta saboda karancin jami’an yan sanda - Kwamishanan yan sanda

Marigayin wanda ba’a riga an samu cikakken bayani akansa ba anyi masa sallar jana’iza a safiyar Assabar yayinda akayi gaggawar garzayawa da wadanda suka samu rauni zuwa babban asibitin Katsina.

Mutane da yawa sunyi hijira daga kauyen, bisa la’akari da cewa ana zargin harin bai rasa dangantaka da kashe wani dan bindiga da kungiyar ‘yan sakai tayi kwana daya kafin kawo harin.

“ Muna da tabbacin cewa harin ramuwace bisa kashe dan uwansu daya da akayi,” a cewar wata majiya data shaidawa wakilinmu.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Katsina, SP Gambo ya tabbatar da aukuwar wannan lamari.

A wani labari mai kama da wannan, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano yace sam babu wani abu tsakanin shi da Sarki Sanusi lamido.

Zancen ya biyo bayan cece-kuce da jama'a keyi na cewa gwamnan yayi hakan ne da gayya ga Sarki Sanusi. Gwamnan ya sake cewa, "Sarki kamata yayi ace yana karkashin shugaban karamar hukuma idan har bukatar ganawa ta taso da shi zai yi magana, kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tsara."

Ba abinda ke tsakanina da Sarki Sanusi, inji Ganduje

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel