Yadda ake duba sakamakon jarabawar JAMB 2019

Yadda ake duba sakamakon jarabawar JAMB 2019

-Ga hanyar duba sakamakon JAMB cikin sauke ba tare da amfani da yanar gizo ba

-Idan har sakamakon jarabawar ya samu matsala zaka gani ta hanyar rubutaccen sako wato SMS

Wannan wata hanyace mafi sauki ga wadanda suka rubuta jarabawar shiga makarantun gaba da sakandare wato JAMB UTME 2019 da zasu iya duba sakamakonsu.

Ku aika da rubutaccen sako zuwa 55019 ta hanyar amfani da lambar wayar da kukayi rajista da ita.

Babu bukatar sai mutum yaje cibiyar CBT ko kuma inda ake aiki da yanar gizo domin duba wannan sakamako.

Yadda ake duba sakamakon jarabawar JAMB 2019

Yadda ake duba sakamakon jarabawar JAMB 2019
Source: UGC

KU KARANTA:Ba abinda ke tsakanina da Sarki Sanusi, inji Ganduje

Wadanda basu zauna rubuta jarabawar ba ko kuma aka soke jarabawartasu za’a sanar dasu hakan.

Ga kadan daga cikin amsoshin da mutum kan iya samun baya ya aika da rubataccen sakon:

1. Idan mutum yayi amfani da lambar da bitace yayi rajista da ita ba, za’a fada masa: “ Wannan lambar batayi rejista ba.”

2. Wanda kuma sakamakonsa kenan zai samu sako kamar haka: “ Yallabai wane, sakamakon ka/ki ( ainihin abinda ka samu a jarabawar zai bayyana)”.

3. Idan kuma an rike sakamakon ne, zaku ga “ An rike wannan sakamakon”.

4. Idan kuma sakamakon mutum bai kammala ba zai ga: “ An rike sakamakon muna bukatar ka sake daura wasu takardunka a shafinmu.”

5. Idan kuma mutum bai zauna jarabawar ba, “ Wannan bai zauna ba.”

6. Idan kuma mutum bai zauna ba kuma an soke masa lambar rajista za’a sanar dashi hakan.

7. “ Shiga dakin jarabawa ba bisa ka’ida ba”, shine abinda wanda ya shiga wurin jarabawar ba a kan doka ba zai gani.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel