Yanzu Yanzu: Sanusi ya samu mukami a majalisar dinkin duniya kwana daya bayan an kacaccala masarautarsa

Yanzu Yanzu: Sanusi ya samu mukami a majalisar dinkin duniya kwana daya bayan an kacaccala masarautarsa

Majalisar dinkin barakar duniya ta nada Sarki Sanusi a matsayin mamba na kwamitin masu sanya ido kan sabbin muradodin ci gaba na wannan qarni (SDG).

Babban sakataren majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres yayi sanarwar ta hannun kakakinsa, Mista Farhan Haq, a wani taron manema labarai a birnin New York a ranar Alhamis, 9 ga watan Mayu.

Wakilan SDG sun kunshi manyan mutane 17 da suka jajirce wajen “wayar da kan jama’a, karfafa kudirori nagartattu, da kuma daukaka ayyukan ci gaba cikin sauri."

Yanzu Yanzu: Sanusi ya samu mukami a majalisar dinkin duniya kwana daya bayan an kacaccala masarautarsa

Yanzu Yanzu: Sanusi ya samu mukami a majalisar dinkin duniya kwana daya bayan an kacaccala masarautarsa
Source: Twitter

Sanusi na daya daga cikin sabbin mambobin kungiyar shida, wanda shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo-Addo da Firaye Ministan Norway, Ms Erna Solberg ke jagoranta.

Sauran mambobin kungiyar biyar sun hada da Hindou Ibrahim na Chad, Dia Mirza na India, Edward Ndopu na Kasar Afrika ya kudu, Nadia Murad na Iraq da kuma Marta Vieira da Silva na Brazil.

Haq yace sabbin mambobin kungiyar shida za su ci gaba daga inda tsoffin mambobin kungiyar shida suka tsaya.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Majalisar dokokin jihar Kano karkashin jagorancin kakakin majalisar Rt. Hon Alhassan Rurum ta amince da kafa sababbin masarautu guda hudu a fadin jihar Kano.

KU KARANTA KUMA: Badakalar kudi: Gwamnatin Kano ta titsiye hadimin Sarki Sanusi

"Ba a samu wadanda suka nuna rashin amincewar su ba a dakin majalisar. Sai dai akwai wadanda suka dinga fita daga majalisar wadanda alamu ke nuna cewa ba su ji dadin dokar ba," wani dan majalisar wanda ya bukaci a boye sunansa, ya bayyanawa manema labarai.

Garuruwan da dokar ta yadda su yi sarautar sun hada da Masarautar Kano, Masarautar Rano, Masarautar Gaya, Masarautar Karaye da kuma Masarautar Bichi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel