Masarautun Kano: Dan majalisa mai wakiltar Dambatta ya fice daga zaman majalisa

Masarautun Kano: Dan majalisa mai wakiltar Dambatta ya fice daga zaman majalisa

- Ya fice daga zaman saboda babu daidaitawa a cikin tsarin rarraba masarautar.

- “Babu adalci a kirkirar masarautar Bichi shi ya sa na fice daga zaman don nuna rashin jin dadi na, saboda majalisa ba ta girmama abunda na hanga ba.”

Wani dan majalisa mai wakilatar karamar hukumar mulkin danbatta, Alhaji Hafizu Sani Mai Daji ya fice daga zaman majalisa a matsayin nuna rashin goyon baya a kudurin karkatsa masarautar Kano.

Mai Daji ya fada ma manema labarai ranar Larba cewa ya fice daga zaman saboda babu daidaitawa a cikin tsarin rarraba masarautar.

Yace, “ba a ba karamar hukumar mulkin Dambatta muhimmancin da ya dace ba, Dambatta ya kamata a ba masarauta ba Bichi ba. Saboda"

Uban kasar Dambatta shine mafi dadewa a Kano kuma yana cikin masu nada sarki”.

Babu adalci a kirkirar masarautar Bichi shi ya sa na fice daga zaman don nuna rashin jin dadi na, saboda majalisa ba ta girmama abunda na hanga ba.”

Idan masu karatu ba su manta ba legit.ng ta kawo maku rahoton cewa wani ‘dan majalisa, Salisu Ibrahim Chambers, shi ne ya fara kawo wannan kudiri a gaban zauren majalisar inda yake neman sauran Abokan aikinsa su amince da hakan.

Wannan kudiri ya jawo ce-ce-ku-cen gaske a zaman da aka yi. Dole dai majalisar ta dakatar da zaman zuwa lokaci na gaba bayan ganin ‘yan majalisar jihar sun gaza cin ma matsaya inda wasu ke nuna goyon bayan su a kan wannan magana, yayin da wasu ‘yan majalisar su ka tubure su kace a’a.

KU KARANTA: Siyasar Kano: Majalisa na so a tsaga Masarautar Kasar

Wadannan sababbin Sarakuna da ake so a nada a kasar Gaya, Karaye, Bichi da Rano, za su sa yawan Sarakunan jihar Kano su zama 5. Kowane Sarki zai samu mukamin Sarki mai iko mai matakin farko a kasar ne idan hakan ta tabbata.

Masana harkar siyasa sun ce wannan shiri da majalisar dokokin ta kawo, bai rasa nasaba da rikicin da ake yi tsakanin gwamnatin jihar Kano da kuma Mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi II wanda ake ganin bai tare da gwamnati. Tsohon Kakakin majalisar Kano, Alhaji Isiyaku Ali Danja, ya nuna rashin amincewar sa da wannan kudiri inda yayi kira ga sauran ‘yan majalisa su guji taba gidan Sarautar. Wannan ya sa majalisa ta bada lokaci domin a sake duba lamarin. Siyasar Kano Majalisa na so a tsaga Masarautar Kasar Kano

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel