Najeriya shugabanni marasa ubangida take bukata, a cewar Dogara

Najeriya shugabanni marasa ubangida take bukata, a cewar Dogara

-Kakakin majalisar wakilai, bai aminta da cewa cin hanci da rashawa shine ya hana kasar nan cigaba ba

-Dogara ya shawarci kungiyar majalisar matasa da su kasance shugabanni nagari domin kawo cigaban kasar nan

Kakakin majilisar wakilai Yakubu Dogara a ranar Talata yace Najeriya nada bukatar shugabanni wadanda zasu maida hankali fannin bukatun jama’arsu amma ba masu yin biyayya ga masu gidansu ba.

Dogara bai aminta da fadar akasarin mutane ba cewa matsalar Najeriya ta ta’allakane akan cin hanci da rashawa kadai. Inda yake cewa “ babbar matsalar kasar nan itace rashin nagartattun shugabanni wanda ya haifar da cin hanci da kuma zalunci a wannan kasa.”

Najeriya shugabanni marasa ubangida take bukata, a cewar Dogara

Kakakin majalisa, Yakubu Dogara
Source: UGC

KU KARANTA:Ina sane da nauyin dake kaina, kuma ina sane da abinda nake yi sarai – Shugaba Buhari

Dogara yayi wannan batun ne a Abuja, akalla kwanaki uku kafin Gwamna El-Rufai ya shaidawa jihar Legas yadda zasu iya magance siyasar ubangida yayinda ya halarci wani taro a jihar ta Legas.

A wata takarda wacce ya gabatar wurin taron da kungiyar majalisar matasa ta shirya, Dogara ya shawarci matasa dasu guji amfani da karfi yayinda suka kasance suna rike da madafin iko.

Yace “ babbar matsalar Najeriya itace abinda ya shafi jagoranci. Sam ban aminta da fadar masu cewa handamar dukiya da rashawa sune matsalar kasar nan ba. Hakikanin matsalr ta samo asaline daga rashin nagartar shugabanninmu.” Inji kakakin majalisar.

Samun shugabanni masu nagarta shine zai ba kasarmu damar samun cigaban da muke bukata. Jagoranci na da wahala amma idan kuna gudanar da ayyukanku ku tuna cewa mutane kuke wakilta don haka nauyinsu na bisa kanku wannan shi zai baku damar kwatanta adalci. A cewar Dogara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel