Rikicin Zamfara: Rudunar sojin sama ta kashe yan bindiga 20 a dajin Zamfara

Rikicin Zamfara: Rudunar sojin sama ta kashe yan bindiga 20 a dajin Zamfara

-Mayakan Operation diran mikiya tayi nasarar hallaka yan bindiga 20 a wani harin da ta kai dajin Rugu na jihar Zamfara

-Kakakin rundunar sojin sama, Ibikunle Daramola ya tabbatar da gaskiyar wannan lamari

Mayakan Operation Diran Mikiya na rundunar sojin sama ta Najeriya a jiya Talata sun kai farmaki a sansanin yan bidiga dake dajin Rugu inda daya daga cikin jagororinsu wato Alhaji Lawal yake da zama, yayinda sukayi nasarar kashe yaransa guda 20.

Kakakin rundunar sojin saman, Komodo Ibikunle Daramola a zance da ya fito daga wajen shi cewa yayi, sun kwashi tsawon lokaci suna bibiyar wannan sansani tun 26 ga watan Afrilu. Bayan gudanar da bincike ta hanyar amfani da bayanan sirri muka tabbatar cewa Lawal ya kafa sansani cikin dajin na Rugu.

Rikicin Zamfara: Rudunar sojin sama ta kashe yan bindiga 20 a dajin Zamfara

Rikicin Zamfara: Rudunar sojin sama ta kashe yan bindiga 20 a dajin Zamfara
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Kotun daukaka kara ta baiwa Modibbo nasara a zaben majalisar dokoki

Daramola ya kara da cewa, " Lawal ya cigaba da amfani da damarshi yana kai hari zuwa ga mutanen dake kauyuka kai harma da jami’an tsaro daga nan sansanin na shi.

"Bayan mun kammala duk wani bincike namu, mun aika mashi da jiragen yaki guda biyu domin ragargazar sansanin na shi kuma mun samu nasara." A cewar Daramola Ibikunle.

A wani labarin makamancin wannan, sufeton yan sanda ya bada umurnin janye jami'an yan sanda masu tsaro wasu daidaikun mutane.

Babban sufeton yan sanda ya bada umarnin janye masu tsaron wasu daidaikun mutane

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel