Matar Obasanjo ta zarge shi da aika masu kisan gilla su kashe danta

Matar Obasanjo ta zarge shi da aika masu kisan gilla su kashe danta

- Matar Obasanjo ta zarge shi da aika masu kisan gilla su kashe danta

- Wannan babbar barazana ce ‘yansanda su taimake mu

Mrs. Taiwo Obasanjo, matar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ta yi zargin cewa a halin yanzu ita da danta suna cikin halin tashin hankali saboda mara wa shugaban kasa Muhammadu Buhari da suka yi a zaben da ya gabata.

Matar Obasanjo tace majiya mai karfi ta tabbatar mata cewa wani wanda bai ji dadin marawa shugaba Buhari da ta yi ba ya tura ma ita da danta masu kisan gilla.

A ta bakinta, ta samu sahihin bayanin cewa ana zargin Cif Olusegun Obasanjo da biyan masu kisan gilla dake biye da ita da danta.

KU KARANTA: Babban Bankin Najeriya ya fara binciken asusun ajiyar masu fasa kaurin kayayyakin sawa

Matar ta Obasanjo tace masu kisan gillar suna shirin kashe ta kuma su batar da sawu don mutane su dauka aikin ‘yan fashi ne.

Ta kuma yi zargin cewa abu na biyu da za su yi shine kashe Olujonwo a wani shiri mai kama da harin ‘yan fashi.

Tace: “Ina son duniya ta san cewa rayuwata da ta dana Olujonwo, na cikin hadari saboda goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari da muka yi a lokacin zaben da ya gabata.

“Ina rokon duk wani wanda ya san Baba don Allah ya fada masa kar ya kashe ni da dana. Ba laifi ba ne don mun goyi bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari da har zai sa a kashe mu”

“Kuma ina rokon jami’an tsaro da su cece mu.”

“Wannan babbar barazana ce ‘yansanda su taimake mu, wannan ba wani abun neman suna ne ba.”

Kokarin da aka yi na jin ta bakin Obasanjo ya citura, kuma an kira wayar mai yi masa hidima ba a same shi ba.

Amma wata majiya ta kusa da Obasanjo tace ba ya kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel